Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-14 18:29:49    
Kasar Sin za ta kara zuba kudi kan ayyukan ba da taimakon agaji da warkar da yara nakasassu

cri
A ran 14 ga wata, mataimakiyar shugaban zaunannen kwamitin majalisar dokoki ta kasar Sin Madam Gu Xiulian ta bayyana cewa, kasar Sin za ta kara zuba kudi kan ayyukan ba da taimakon agaji da warkar da yara nakasassu.

Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta kira taro a ranar a birnin Beijing domin yin nazari kan sa kaimi ga ayyukan warkar da yara nakasassu. A gun taron, Madam Gu ta bukaci wurare daban daban na kasar Sin da su shigad da ayyukan warkar da yara nakasassu a cikin muhimman shirye-shiryen raya tattalin arziki da zaman rayuwa domin warware matsalolin da ke cikin ayyukan warkar da yara nakasassu, da kafa wani tsarin kula da ayyukan warkar da yara nakasassu domin sa kaimi ga tsara da gyara dokokin da abin ya shafa. A waje daya kuma ta bukaci da a ci gaba da karfafa gwiwar mutane na sassa daban daban na kasar Sin domin su ba da taimako ga yara nakasassu.(Kande Gao)