A ran 14 ga wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labaru a nan birnin Beijing, inda jami'ai wadanda suke shugabantar ma'aikatar al'adu ta kasar Sin da babbar hukumar kula da harkokin film da rediyo kuma da talibijin da babbar hukumar kula da harkokin dab'i ta kasar Sin sun ba da amsoshi filla filla ga tambayoyin da manema labaru suka yi musu kan Shiri na 11 na shekaru biyar-biyar don raya al'adun kasar Sin.
A ran 13 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta bayar da "Tsarin 11 na shekaru biyar-biyar don raya al'adun kasar Sin", inda aka bayyana tunanin jagoranci da za a bi da burin neman bunkasuwa da za a cimmawa kuma da muhamman ayyukan da za a yi lokacin da ake aiwatar da wannan tsari. Sun Jiazheng, ministan al'adun kasar Sin yana ganin cewa, wannan tsari yana da muhimmanci sosai ga neman bunkasuwar duk al'ummar kasar Sin a nan gaba. Mr. Sun ya ce, "Wannan tsarin farko ne da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta tsara musamman domin raya al'adun kasar Sin bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin. Wannan tsari yana daidai da bukatar neman bunkasuwar tattalin arziki da siyasa da al'adu cikin halin daidaito a cikin sabon karnin da muke ciki. Wannan kuma wani muhimmin mataki ne da aka dauka domin raya zaman al'umma cikin lumana kuma da yunkurin cimma burin raya wata zaman al'umma wadatace daga duk fannoni."
Gwamnatin kasar Sin ta bayar da wannan tsari ne domin ba da amsa ga manufofin raya zaman al'umma cikin lumana bisa moriyar dan Adam. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, wasu manazarta na kasar Sin sun yi shakka kan manufofin mai da hankali kan bunkasuwar tattalin arziki da gwamnatocin matakai daban-daban na kasar Sin suka dauka. Sun bayyana cewa, domin an fi mai da hankali kan bunkasuwar tattalin arziki kawai, an riga an haddasa matsaloli iri iri.
A cikin 'yan shekarun da suka wuce, domin kasar Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri sosai, yanzu, a manyan biranen kasar Sin, ana bayar da abubuwan al'adu da kayayyakin da ake bukata kamar yadda kasashe masu arziki suka bayar. Amma a yankunan da ke nesa da garuruwa da yankunan yammacin kasar Sin, ba a samu bunkasuwar tattalin arziki sosai ba domin sharudan halittu da dalilan da suka kasance a tarihi. Jama'ar da suke da zama a wadannan wurare ba su iya samun abubuwa da kayayyakin al'adu isassu ba. Sabo da haka, a cikin wannan tsarin da aka bayar a jiya, an jaddada cewa, za a kara saurin raya abubuwan film da na rediyo kuma da na talibijin. Madam Zhao Shi, mataimakiyar babban direktan hukumar film da rediyo da talibijin ta kasar Sin ta ce, lokacin da gwamnatin kasar Sin take mai da hankali wajen raya sana'o'in film da rediyo da talibijin, za ta kuma mai da hankali wajen yin wasu shirye-shiryen film da rediyo da na talibijin don jama'a, musamman za a kara samar wa mutane wadanda suke da zama a kauyuka abubuwan da suke bukata. Ta ce, (??????)
"Za a aiwatar da ayyuka 3 ga kauyuka domin kawar da matsalolin da ba a iya kallon film da samun shirye-shiryen rediyo da na talibijin cikin sauki ba a kauyuka. Sa'an nan kuma, za a kara kyautata ayyukan yau da kullum da sharudan samun shirye-shiryen rediyo da na talibijin a yankunan yammacin kasar Sin da yankunan da mutanen kananan kabilun kasar suke da zama."
Bugu da kari kuma, wannan tsarin raya al'adun kasar Sin yana da wani halin musamman, wato an fi mai da hankali kan yin amfani da sabbin fasahohin zamani lokacin da ake raya al'adun kasar Sin. Alal misali, an nemi a kara yin amfani da fasahar digital lokacin da ake tsara da watsa shirye-shiryen rediyo da na talibijin, kuma a yi amfani da fasahar digital a dakunan litattafai da dai sauransu. Sun Jiazheng, ministan al'adun kasar Sin ya ce, za a yi kokari domin kawar da bambancin fasahohin digital da ke kasancewa a tsakanin birane da kauyuka. Mr. Sun ya ce, "A babban dakin litattafai na kasar Sin, za a kafa wata cibiyar musayar labarun al'adu ta kasar Sin. Sa'an nan kuma za a kafa sassanta a yankuna daban-daban. Sakamakon haka, jama'ar duk kasar Sin za su iya samun labarun al'adu da suke bukata ta wannan cibiyar da tsarinta." (Sanusi Chen)
|