Ran 14 ga wata, ma'aikatar kula da harkokin jama'ar kasar Sin ta sanar da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta tabbatar da magance matsalar rashin wurin kwana da wadanda bala'i ya rutsa da su ke fuskanta kafin lokacin hunturu.
A ran nan, ma'aikatar kula da harkokin jama'ar kasar ta sake kebe kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan miliyan 137 zuwa larduna 6 wato Fujian da Zhejiang da Jiangxi da Jilin da Yunnan da kuma Qinghai don taimakawa wajen sake gina gidaje a wuraren da suka sha fama da wahalar bala'in ambaliyar ruwa da kuma girgizar kasa.
Tun daga farkon wannan shekara har zuwa yanzu, kasar Sin ta gamu da munanan bala'o'i daga Indallahi. Hukumomin da abin ya shafa sun riga sun kebe kudin agaji da yawansa ya kai kudin Sin fiye da yuan biliyan 3 zuwa wuraren da ke sha fama da wahaloli a sakamakon bala'i. A watan Nuwamba mai zuwa, ma'aikatar kula da harkokin jama'ar kasar za ta hada kanta da bangarorin da abin ya shafa wajen yin kira ga al'ummar kasar da su ba da gudummowar kudi da kayayyaki ga mutanen da ke sha fama da bala'i.(Tasallah)
|