Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-14 15:19:41    
Yawan kudin agaji da kasar Sin ta bayar a bana ya kai kusan yuan biliyan 3.1

cri
A shekarar da muke ciki, kasar Sin ta gamu da bala'o'i iri iri masu tsanani daga indallahi, kuma ya zuwa yanzu, sassan da abin ya shafa na gwamnatin kasar Sin, sun rigaya sun bayar da kudaden agaji da yawansu ya kai kusan biliyan 3.1 ga shiyyoyin da bala'in ya shafa, don taimaka wa lardunan da bala'in ya shafa wajen ba da agajin gaggawa da kuma sake farfado da yankunan.

Mataimakin ministan harkokin gida na kasar Sin, Li Liguo ya ce, a shekarar da muke ciki, kasar Sin ta gamu da bala'i mai tsanani da ba a taba ga irinsa ba tun shekarar 1998. Bisa kidayar da aka yi, an ce, ya zuwa ran 11 ga watan nan da muke ciki, bala'o'in sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 2295, yayin da wasu 564 suka bace. Ban da wannan kuma, an yi asarar dukiyoyi da yawansu ya kai kudin Sin yuan sama da biliyan 190.