Ya zuwa yanzu, akwai kamfanonin inshora sama da 40 na kasashen waje wadanda ke gudanar da harkokinsu a kasuwannin inshora na kasar Sin.
Ran 13 ga wata, Malam Li Kemu, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin inshora ta kasar Sin ya yi jawabi a gun taron dandalin tattaunawa kan harkokin kudi na duniya na karo na uku, da aka yi a birnin Beijing, inda ya bayyana cewa, bayan da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO a cikin shekaru biyar da suka gabata, kamfanonin inshora na kasashen waje wadanda ke gudanar da harkokinsu a kasuwannin kasar Sin sun sami bunkasuwa yadda ya kamata. Yanzu, ko da yake yawan kudaden inshora da wadannan kamfanoni suka samu ba su da yawa sosai a kasar Sin, amma duk da haka wasu daga cikinsu sun sami bunkasuwa da sauri a wasu manyan birane na kasar Sin kamar birnin Guangzhou da birnin Shanghai da sauransu. (Halilu)
|