|
Ran 13 ga wata, ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Italiya ta bayyana cewa, a wannan rana, kasashen Italiya da Libya sun cimma yarjejeniyar inganta hadin guiwa a tsakaninsu, don yaki da fataucin bakin haure daga kasar Libya zuwa kasar Italiya.
Ran 12 ga wata a birnin Roma, jami'an kasashen biyu sun gana tsakaninsu, inda suka tattauna kan batun inganta hadin guiwa don yaki da fataucin bakin haure. A ran 13 ga wta, wani jami'in ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Italiya ya bayyana cewa, bisa yarjejeniyar da aka daddale a tsakanin kasashen biyu, Italiya da Libya za su hada guiwa, su yi sintiri a bakin teku na kasar Libya. Ka zalika gwamnatin kasar Libya za ta aika da 'yan sandanta zuwa kasar Italiya don taimaka wa hukumar 'yan sanda ta kasar Italiya wajen yaki da masu fataucin bakin haure. (Halilu)
|