|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-09-13 20:40:06
|
 |
Kungiyar kwatago ta kasar Sin tana mai da kungiyoyin kwadago ta Afrika kamar abokanta
cri
Ran 13 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Wang Zhaoguo, shugaban babbar kungiyar kwatago ta kasar Sin ya bayyana cewa, kullum kungiyar kwadago tana mai da kungiyoyin kwadago ta Afrika kamar abokan amincinta, ya yi yabo sosai ga kungiyoyin kwadago na kasashen Afrika, sabo da suna tsayawa kan manufa, da matsayi mai adalci a cikin harkokin kungiyar kwadago na duniya, da kuma goyon baya da suke nunawa kungiyar kwadago ta kasar Sin da zuciya daya.
Mr. Wang Zhaoguo ya yi wannan bayani ne, a lokacin da yake ganawa da wakilan da suke hallartar taron tattaunawa na shugabannin kungiyoyin kwadago na kasashen Afrika, masu yin amfani da harshen Turanci da aka shirya a kasar Sin.
Mr. Wang Zhaoguo ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen Afrika sahihan abokan juna ne da ke iya shan wahala tare. Ya hakake cewa, ko shakka babu, ziyarar da shugabannin kungiyoyin kwadago na kasashen Afrika su ke yi, za ta samar da bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kungiyoyin kwadago na kasar Sin da kasashen Afrika a duk fannoni.
Manyan shugabannin kungiyoyin kwadago da suka zo daga kasashen Afrika 17 sun bayyana cewa, kungiyoyin kwadago na kasashen Afrika sun yi godiya ga taimakon da gwamnati da kungiyar kwadago na kasar Sin suka ba su, suna fatan yin kokari tare da kungiyar kwadago ta kasar Sin, domin samar da kyakkyawan hadin kai da da ke tsakanin bangarorin biyu zuwa wani sabon matsayi. (Bilkisu)
|
|
|