Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-13 17:29:31    
Takardun masu sauraronmu

cri

Kwanan baya, mun sami wasikar E-mail daga wajen mai sauraronmu Sani Mohammed, mazaunin Musa Umar Street, Mando, Kaduna ta kasar Nijeriya, inda ya ce, na rubuto ne domin in nuna jin dadi na game da shirye-shiryenku. Sa'an nan kuma da farin cikina game da nuna sha'awarku kasar Sin ga harshen Hausa, har ma ta samar da fili a gidan rediyonta, domin gabatar da shirye-shiryen Hausa. Mun gode kuma Allah ya bar zumunci tsakaninmu, amin.

Sa'an nan kuma, shafinku na internet, gaskiya ya kayatar da ni. Hasali ma dai, wannan shafi wani dakin karatu ne inda mutum zai iya tuntuba domin samun bayanai a ko wane lokaci, an tsara shi da kyau. Za mu ci gaba da ba ku goyon baya ta hanyar saurare da kuma aiko da sakonni da shawarwari na karfafa gwiwa.

Muna godiya kwarai da gaske ga malam Sani Mohammed da ya aiko mana wannan wasika mai karfafa gwiwa. Za mu kara kokartawa don jin dadinku. Muna kuma fatan malam Sani Mohammed zai ci gaba da aiko mana sakonni, ka ba mu shawarwari, ta yadda za mu kara inganta shirye-shiryenmu da kuma shafinmu na internet. Da fatan Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.

Sai kuma Dalhatu Manjos Gobir Samaru Zaria daga jihar Kaduna da Mustapha mai hoto bakin makarantar boko Danja jihar Katsina da kuma Magaji sarki Hayin dogo Samaru Zaria sun hada gwiwa sun rubuto mana cewa, muna shaida muku cewa, muna jin dadin dukan shirye-shiryenku. Gaskiya muna farin ciki da samun wannan sakonku, sabo da kun san babban burinmu shi ne jin dadinku. Da fatan za ku ci gaba da ba mu tallafi da goyon baya, ta yadda za mu kara samun ci gaba.

Sa'an nan daga jihar Kaduna, mai sauraronmu Mannir Ali Faki ya rubuto mana cewa, ni ma na shiga gasar kacici-kacicinku, to, na ji shiru ne, shi ya sa na rubuto na ji ko ba ku ga amsa ta ba ne? in kun gani mene ne sakamakon nawa amsar? A hakika, bayan da muka bude gasar kacici-kacici a wannan shekara, mun samu sakonni masu yawa daga masu sauraronmu, amma ba za mu kawo karshen gasar ba sai zuwa karshen watan nan da muke ciki. Shi ya sa, masu sauraronmu, sai ku yi hakuri, bayan da muka kawo karshen gasar, za mu fitar da wadanda suka fi kwarewa a gasar, da kuma bayyana muku sakamakon nan da nan, da fatan za ku kara kokari, don cimma nasarori a gasar.

Har wa yau kuma, mai sauraronmu Amadou daga kasar Belgium, ya rubuto mana cewa, ina so ku ba ni bayanin yadda zan yi in sauraronku? To, malam Amadou, ina tsamanin kana zaune ne a kasar Belgium, shi ya sa watakila ba damar ka same shirye-shiryenmu ta hanyar rediyo. Sabo da muna watsa shirye-shiryenmu da harshen Hausa ne ga kasashen Nijeriya da Nijer da Kamaru da Chadi da dai sauran kasashen da ke yammacin Afirka. Amma ba damuwa, fasahar zamani ta samar maka saukin kama mu ta hanyar internet, ko yaushe kuma duk inda kake, kana iya sauraron labarunmu da dumi duminsu da dai sauran shirye-shiryenmu masu kayatarwa daga shafinmu na internet, wato abin da muke kira online listening ke nan, kuma wannan adireshinmu na internet shi ne www.cri.com.cn. Da fatan za ka ji dadin shafinmu na internet.

Sai kuma malam Abba Mohammed, mai sauraronmu a ko da yaushe daga birnin Kano na kasar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, akwai wata shawara da zan ba ku, wato ko zai yiwu ku samar da wani shiri a kan musulunci a kasar Sin? Malam Abba, da farko dai, ina so in nuna godiyarmu ga sauraron shirye-shiryenmu da ka kan yi a kullum da kuma goyon bayan da ka ba mu. Game da wannan shawarar da ka ba mu, na yi farin ciki da sanar da kai cewa, yanzu muna da wannan shiri, wato musulunci a kasar Sin, wanda malama Bilkisu ce ke gabatarwa a duk ranakun Jumma'a, dangane da zaman rayuwar musulmi a nan kasar Sin. Tare da fatan shirin ba zai wuce ka ba, kuma za ka ji dadin shirin. Muna kuma fatan za ka ba mu ra'ayoyinka da shawarwari a kan shirin nan bayan da ka saurara.

Bayan haka, mun kuma sami sakonni daga wajen kungiyar masu sauraronmu ta jihar Gombe ta kasar Nijeriya da malam Abba Garba, mazaunin garin Gumel na jihar Jigawa da malam Adamu Jibril mai Kantuna Inkiya Danjuma Jatau Unguwan Nungu na jihar Kaduna da malami alh.Yusuf da dai sauran masu sauraronmu masu yawa wadanda a nan ba za mu iya fada sunayensu ba. Muna so mu tabbatar muku da cewa, sakonninku mun riga mun samu, kuma muna godiya matuka ga wadannan sakonninku masu karfafa gwiwa da shawarwarinku masu kyau. Muna fatan za ku ci gaba da ba mu tallafi da goyon baya.(Lubabatu)