Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-13 16:56:56    
Wani mutum na zamanin da na kasar Sin mai suna Zhu Yuanzhang

cri

Zhu Yuanzhang yana daya daga cikin sarakunan da suke soma kafa daulolinsu. Amma daga cikinsu, Zhu Yuanzhang na da tarihin mamaki da ke fama da talauci sosai a cikin mawuyacin hali. Ya kware sosai wajen daidaita matsaloli tare da kasancewa cikin tunanin hangen nesa sosai, ya yi aiki wurjanjan wajen harkokin siyasa, shi kansa ya daidaita kowane aiki ,shi ne sarkin da ba a kan samu ba wajen ba da gudumowa da yawa a tarihin kasar Sin.

An haifi Zhu Yuanzhang a shekarar 1328 a garin Fengyan na lardin Anhui, iyayensa sun rasu tun lokacin da yake karami, gidansu ya yi fama da talauci sosai da sosai , ya taba zuwa karatu a makaranta, amma sa'anan kuma ya bar makaranta bisa sakamakon rashin biyan kudin makaranta, ya yi aikin kiwon shanu domin ciyar da kansa. A shekarar 1334, Garin Zhu Yuanzhang ya gamu da bala'in fari da ba a taba ganin irinsu ba, fari sun cinye amfanin gona duka duka, mutane da yawa sun mutu bisa sanadiyar 'yunwa. A lokacin da ya cika shekaru 16 da haihuwa, ya ga tilas ne ya fita waje ya zama wanda ke bautawar addinin Buddah, ya zama maroki, Ya kuma yin zaman galabaita a cikin wasu shekaru a wurare da yawa. Ta hakan ya sa shi bude idannunsa, kuma ya kara karfin zuciyarsa wajen zaman rayuwa.

Zhu Yuanzhang ya yi zaman rayuwa a karshen daular Yuan. Kabilar Mongoliya ce ta yi mulkinta a daular Yuan. Dayake masu mulkin daular sun nuna bambancin kabila da aiwatar da manufar mulkin danniya , shi ya sa mutane suka yi ta yin tawaye daya bayan daya. Sai Zhu Yuanzhang da ke da shekaru 24 da haihuwa ya shiga cikin rundunar sojojin 'yan tawaye. Dayake ya yi jaruntaka da fid da tsoron kome wajen yaki, sai a kai a kai ne ya sami mukami. Daga baya, Zhu Yuanzhang ya kafa dakarunsa na kansa, daga nan ne aka sake rubuta tarihin kasar Sin.

A shekarar 1368, Zhu Yuanzhang ya kafa daular Ming, kuma ya zama sarkin daular.

Yayin da yake mulkin daularsa, ya sami fasahohi da yawa daga daular Yuan wajen samun hasarar mulki, ya yi gyare-gyare da yawa a kan tsarin siyasa, ya mallaki ikon mulkin kasa a cikin hannunsa shi da kansa kawai. Kuma shi kansa ya daidaita ayyukan kasa da yawa. Amma ba a iya kayyade ikonsa ba, ya iya yin kome da kome yadda ya ga dama, kuma ya yi almubazaranci sosai, wannan ya kawo batutuwan zamantakewar al'umma masu tsanani sosai.

Zhu Yuanzhang ya san talauci mai tsanani sosai da jama'a suka sha, duk saboda shi kansa ya fito daga wajen jama'a masu fama da talauci. Bayan da ya hau kan kujerar mulki, ya mai da muhimmanci ga yin tsimi da abubuwa da yin zaman rayuwa tamkar yadda kowa yake yi. Mun sami labari cewa, wani jami'in wurin ya yi fatan yi wa sarki fadanci , shi ya sa ya mika wa sarki wani gadon da aka yi da zinariya, amma ba zato ba tsammani Zhu Yuanzhang ya yi fushi sosai, ya ba da umurnin murkushe gadon nan, kai ,ba shi kadai ya yi tsimi sosai ba, har ma ya bukaci sauran mutane da suka yi tsimi. Ya kuma tsara manufofin tattalin arzikin noma da suka dace da halin da manoma suke ciki, shi ya sa kasar ta shiga halin bunkasuwa na kasancewar zaman lafiya da wadatuwa.

Amma abin bakin ciki shi ne, a karshen rayuwarsa a duniya, Zhu Yuanzhang ya maido da harkokin kasa tamkar abubuwansa na kansa, ya kashe jami'ansa bisa laifufukan da ba su yi ba, ya kuma kashe masu fasahohi wato bokaye da yawa ba gaira ba dalili, wannan ya bata ran jami'an gwamnati da jama'a sosai.

Zhu Yuanzhang yana da rai har shekaru 71 a duniya, ya hau kujerar mulki cikin shekaru 31. Daular Ming da ya kafa ta kasance cikin shekaru 270 ko fiye. Tattalin arziki da al'adu na daular sun taba samun bunkasuwa da saurin gaske a tarihin mulkin gargajiyar kasar Sin, sun kai matsayin koli a wancan zamani. A lokacin daular, shahararren mai zirga-zirga a tekuna na kasar Sin Zheng He ya yi zirga-zirgar jiragen ruwa a tekuna har sau 7, an kuma wallafa wasu shahararrun littatafai tamkar da da da dai sauransu, yawancin yankunan babbar ganuwar kasar Sin da ke da kilomita fiye da 500 an soma gina su ne a daular Ming, kuma fadar sarakuna na birnin Beijing ita ma an gina ta ne a daular Ming. (Halima)