Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-13 14:39:47    
Mota mai amfani da lantarki za ta ba da gudumuwa ga `tsabtatacen wasannin Olimpic`

cri

Masu sauraro,kamar yadda kuka sani,taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekara ta 2008 shi ne `tsabatatacen wasannin Olimpic`,wato gwamnatin birnin Beijing tana mai da hankali sosai kan aikin gine-ginen muhalli da na kiyaye muhalli.Sabili da haka,ana sanya matukar kokari don rage gurbatar iska da hayakin ababen hawa ke fitarwa.Kwanakin baya ba da dadewa ba,an sami labari daga hukumar da abin ya shafa cewa,dukkan motocin da za a yi amfani da su a gun gasar taron wasannin Olimpic na Beijing na shekara ta 2008 su ne motoci masu kiyaye muhalli,musamman motar dake amfani da lantarki da kasar Sin ta yi nazari da kuma kera ta kanta ba za ta gurbata muhalli ko kadan ba,wato za ta ba da gudumuwa mai muhimmanci ga `tsabtatacen wasannin Olimpic` na Beijing.Yanzu dai bari mu yi bayani kan wannan.

A cikin shekaru goma da suka wuce,a kullum iskar banza da ta fita daga mota tana tsananta kazantar muhalli na Beijing sosai,ya zuwa karshen watan Yuni na bana,gaba daya yawan motocin da birnin Beijing ke mallaka sun riga sun kai miliyan 2 da dubu dari bakwai da talatin,kuma an kimanta cewa za su zarce miliyan 3 kafin karshen wannan shekara.Shi ya sa ana iya cewa,wannan batu matsala mafi tsanani ne dake gabanmu.

Kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya taba yin alkawari cewa,za a yi iyakacin kokari don kyautata ingancin iska ta yadda zai kai ma`aunin da kwamitin wasannin Olimpic na duniya ya tanada.Don haka,dole ne Beijing ta kera mota wadda ba za ta gurbata muhalli ba.

Bisa shirin da aka tsara,za a yi amfani da motoci masu kiyaye muhalli a gun taron wasannin Olimpic.Game da wannan,direktan kwamitin kula da kimiyya da fasaha na birnin Beijing Zhen Jichun ya yi mana bayani cewa,`A gun taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekara ta 2008,gaba daya yawan motocin za a yi amfani da su za su kai wajen dubu daya da dari biyar,dole ne dukkansu motoci masu kiyaye muhalli,wanda a ciki,yawan manyan motocin fasinja da za a yi amfani da su a cibiyar wasannin Olimpic za su kai hamsin.`

Motar lantarki ita ce mota da ake yin amfani da lantarki wajen ba da wuta kawai wato ba mai ba,amma a halin da ake ciki yanzu,irin wannan mota ba ta iya tafi doguwar hanya ba,kuma ana shan wuya wajen cika lantarki.Duk da haka,bayan kokarin da aka yi,an riga an sami ci gaba a fannoni daban daban musamman a kan sabonta fasahohi.Direkta Zhen jichun ya ce:`Fasaharmu fasaha ce ta zamani,ta riga ta kai matsayin ci gaba a duniya.,wato irin wannan fasaha sabuwar fasaha ce a duniya.`

Direkta Zhen Jichun ya ci gaba da cewa,yanzu,kwamitin kula da kimiyya da fasaha na birnin Beijing ya riga ya sami sakamakon fasaha a jere wadanda ke da ikon mallakar ilmi na kansu.Bayan duddubawar kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare na kasar Sin,kuma bayan jarrabawar da aka yi cikin rabin shekara da ta wuce,za a fara yin amfani da irin wannan mota wato babbar motar lantarki ta fasinja a hukunce.Direkta Zhen Jichun ya bayyana cewa,dalilin da ya sa aka sami ci gaba cikin saurin haka shi ne domin goyon bayan da gwamnatin kasar Sin da ta birnin Beijing suke nuna musu.Ya ce:`Kasar Sin tana mai da hankali sosai kan wannan aiki wato aikin yin nazari kan motar lantarki,shi ya sa,yayin da kasar Sin ke gudanar da shirinta na shekaru biyar-biyar na goma,sai ma`aikatar kula da kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta fara gudanar da babban batu na yin nazari kan motar lantarki.Yanzu dai,kokarin da birnin Beijing ke yi wajen kera babbar motar lantaki ta fasinja shi ne goyon bayan da birnin Beijing ke nuna wa `tsabtatacen wasannin Olimpic` da `wasannin Olimpic na kimiyya da fasaha` na shekara ta 2008.Kan wannan kuma,birnin Beijing ya riga ya ware kudin Sin Yuan miliyan dari biyu.`

An yi mana bayani cewa,bayan tattaunawar da aka yi tsakanin kwamitin kimiyya da fasaha na birnin Beijing da kwamitin shirya wasannin Olimpic na birnin Beijing,an tsai da cewa,za a yi amfani da wadannan manyan motocin lantarki na fasinja a cibiyar wasannin Olimpic da sauran muhimman wurare na Beijing,wadanda ke hade da kauyen `yan wasa da kauyen kafofin watsa labarai da wasu muhimman filayen motsa jiki inda za a yi gasanni da sauransu.

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa ku zama lafiya,sai makon gobe war haka in Allah ya kai mu.