Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani kan cewa, Zaman kadanci zai kara hadarin kamuwa da ciwon zuciya, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani mai lakabi haka: Kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha ta zama wani muhimmin batu da ake yin nazari a kai a kasar Sin. To, yanzu ga bayanin.
Bisa bayanin da masu ilmin kimiyya na kasar Danmark suka bayar, an ce, hadarin kamuwa da ciwon zuciya da masu zaman kadanci suke yi zai yi ninki daya idan an kwatanta shi da na masu zama tare da sauran mutane.
Bisa labarin da muka samu daga mujallar Masu Ilmin Kimiyya a ran 13 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki, an ce, manazarta sun bayar da wannan sakamako ne bayan da suka yi bincike kan mazauna dubu 138 da shekarunsu ya kai 30 zuwa 69 da haihuwa da ke shiyyar Arhus ta kasar Danmark. Kuma binciken yana ganin cewa, masu zaman kadanci da shekarunsu ya yi yawa sun fi saukin kamuwa da ciwon zuciya.
Haka kuma bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin mutanen da aka yi musu binciken, mutane 646 sun kamu da ciwon zuciya mai tsanani. Kuma maza da shekarunsu ya zarce 50 da haihuwa da mata da shekarunsu ya wuce 60 da haihuwa wadanda suka yi zaman kadanci sun fi saukin kamuwa da ciwon. Ko da yake yawansu ya kai kashi 8 cikin dari na dukkan mutanen da aka yi musu binciken, amma a cikin mutanen da suka mutu sakamakon ciwon zuciya bayan wata guda, mutanen da yawansu ya kai kashi 96 cikin dari su mutane ne da ke yin zaman kandaci.
Ko da ya ke har yanzu manazarta ba su san ina dalilin da ya sa masu zaman kadanci suka fi saukin kamuwa da ciwon zuciya ba, amma suna ganin cewa, shan taba, da yin abubuwa marasa kyau ga lafiyar jiki, da ba safai su kan yi binciken lafiyar jikinsu ba, da kuma rashin kulawa da gayon baya daga iyalansu su ne muhimman sanadan haifar da ciwon zuciya. Ban da wannan kuma sabo da masu zaman kadanci ba su son karbar taimakon da aka bayar gare su, shi ya sa a cikin zaman yau da kullum, abubuwan da su kan yi ba su yi kamar yadda ya kamata ba.
Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, Kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha ta zama wani muhimmin batu da ake yin nazari a kai a kasar Sin.
|