Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-12 19:18:39    
Tsohon garin Liye da ke yammacin lardin Hunan

cri

Garin Liye yana arewa maso yammacin lardin Hunan na kasar Sin, wanda mafari ne ga 'yan kabilar Tujia. Ma'anar Liye a bakin 'yan kabilar Tujia ita ce kyautata sauruka. An gano fale-falen gorori fiye da dubu 36 na zamanin daular Qin a garin Liye a shekarar 2002 da ta gabata, wadanda gwamnatin zamanin daular Qin ta rubuta takardu a kansu a karni na 2 kafin haihuwar Annabi Isa. Samun fale-falen gorori na zamanin daular Qin ba ma ya kara samar da bayanai wajen yin nazarin zaman daular Qin kawai ba, har ma ya sanya garin Liye ya fara jawo hankulan mutane. Madam Tian Jing, wadda ke ja gorar masu yawon shakatawa, ta bayyana cewa, 'wadannan fale-falen gorori na zaman daular Qin sun shaida cewa, mutane sun fara zama a nan tun daga shekaru dubu dari 1 zuwa shekaru dubu dari 5 da suka wuce, launin fale-falen gorori baki ne yayin da suka fito daga karkashin kasa, amma bayan da aka wanke su da kuma kawar da launi da ruwa daga cikinsu, sun zama yadda suke a lokacin da aka samar da su, ko da yake ba mu san babbagkun Sinnanci da yawa da ke kan wadannan fale-falen gorori ba, amma kakan kakanmu sun rubuta babbaku a bayyane. '

Yanzu tituna 7 da lunguna 6 suna ci gaba da kasancewa a garin Liye, wadanda ke cikin hali mai kyau, kamar su titin Zhongfu na arewa da na kudu da titin Jiangxi da na Daoxiang da sai sauransu, tsawon wadannan tituna da lunguna ya kai mita dubu 2 da dari 5 gaba daya, sa'an nan kuma akwai dakuna fiye da dari 5, wadanda ke nuna salon gine-gine na zamanin daular Ming da Qing da kuma halin musamman na gine-gine na gargajiya na kabilar Tujia, wato an gina su da katako. Mr. Peng Daxian, wani jami'in kula da yawon shakatawa na garin Liye, ya ce, ko wane titi a nan yana da halin musamman da labari nasa, mutane su kan ji dadin saurara. Ya ce, 'alal misali, da can mutanen lardin Jiangxi su ne suka yi ciniki a titin Wanshou. Saboda babu wanda ke zama a nan, shi ya sa mutanen Jiangxi sun zauna a titin Wanshou, a sakamakon bunkasuwar ciniki, yawan mazaunan wurin ya karu sannu a hankali, a karshe dai an samu wani titi. Domin yawancin mazaunan titin Wanshou sun zo ne daga lardin Jiangxi, shi ya sa ana kiran wannan titi titin Jiangxi.'

Titin Zhongfu ya raba tsohon garin nan, gine-ginen da ke cikin titin Zhongfu na arewa sun fi nuna salon gine-gine na kabilar Tujia.

Garin Liye ya taba taka muhimmiyar rawa wajen kasuwanci a cikin tarihi, kamar yadda birnin Nanjing yake a fannin kasuwanci. Kogin Youshui ya kawo wa garin Liye wadata. An shimfida dukan tituna zuwa tashar jiragen ruwa a nan, kuma akwai kantuna manya da kanana masu yawa a gefuna 2, yawancin gine-gine da ke tsaye a gefunan aka gina su da katako, wadanda aka haka zane-zane iri daban daban a cikin kofofi da tagoginsu. An gina wani babbar katanga a ko wadanne dakuna don magance kama gobara.

An shimfida wadannan tsoffin tituna zuwa kogin Youshui. Wani suna daban na wannan kogi shi ne kogin Bai, wanda ke da fadin ruwa, tsaunuka suna tsaye a gefunansa. Jiragen ruwa na su suna kaiwa da kawowa a kan kogin Youshui kullun, haka kuma jiragen ruwa da masu yawon shakatawa ke ciki. Wei Xiaoming, wata budurwa daga lardin Hubei, wadda ke yin yawon shakatawa a nan, ta yi bayanin cewa, tukin jiragen ruwa a kan kogin Youshui ya faranta wa mutane rayuka sosai, musamman ma masu yawon shakatawa sun yi amfani da matukan katako su tuka jiragen ruwa da kansu. Ta ce, (murya ta 6, Wei)

'na ji matukar farin ciki domin ina cikin wani jirgin ruwa da aka tuka shi da matuka, a lokacin da na shiga cikin jirgin ruwa, wata ya fito, tsoffin dakuna suna kan tsaunuka masu nesa, mutane da yawa suna yawo a gabobin kogin. Na yi wasa da ruwa, saboda ruwan kogin Youshui na da tsabta sosai, na ji dadi kwarai.'

Ban da wannan kuma, abinci iri daban daban na garin Liye na da halin musamman, idan ka ziyarci garin Liye, amma ba ka dandana wadannan abinci ba, to, za ka yi da-na-sani.

To, jama'a masu sauraro, karshen shirinmu na yau na yawon shakatawa a kasar Sin ke nan. Ni Tasallah da na gabatar nake cewa, ku huta lafiya, sai mako na gaba, idan Allah ya kaimu.