Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-12 19:14:23    
Babbar kasuwa ta Kashi

cri

A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan babbar kasuwa da ke yankin Kashi na jihar Xinjiang ta kasar Sin, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, tsohon garin Liye da ke yammacin lardin Hunan.(music)

Babbar kasuwa ta Kashi tana cikin yankin Kashi na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cib gashin kanta ta kasar Sin, fadinta ya kai kadada 8.6, wadda kasuwa ce mafi girma a yankin Kashi har ma a duk jihar Xinjiang, ana kiranta 'bikin baje-koli na kayayyaki na yankin Tsakiyar Asiya', ta nuna halin musamman na kananan kabilu da na wurin a bayyane.

Babbar kasuwa ta Kashi tana da shekaru fiye da dubu 2 da haihuwa, da can an mayar da ita a matsayin kasuwa mafi girma a duk yankin Asiya. Akwai kantuna fiye da dubu 5 a cikin wannan babbar kasuwa, inda ake sayar da kayayyaki iri-iri kimanin dubu guda. Birnin Kashi dadadden birni ne a fuskar tarihi da al'adu a kan hanyar siliki ta gargajiya, haka kuma wuri ne da 'yan kasuwa ke rarraba kayayyakinsu, a can can can da 'yan kasuwa da ke zuwa daga birnin Xi'an su kan taru a nan.

Tun bayan da aka bude tashoshin bincike na Hong Qi La Fu da kuma Tu Er Ga Te, an bude hanyoyin shigowa da kayayyaki daga kasashen duniya, masu yawon shakatawa da 'yan kasuwa da kuma ayarinsu na kasashen waje masu yawa suna sayar da kayayyakin kasashen waje da yawa a babbar kasuwa ta Kashi, sa'an nan kuma, su kan sayi kayayyakin kasar Sin da yawa. Ayarin 'yan kasuwa da suke kaiwa da kawowa a tsakanin babban yankin kasar Sin da kasashen Kungiyar Tarayyar Kasashe Masu 'Yancin Kai da kasashen Pakistan da Yammacin Asiya suna yin ciniki a nan.

A ko wace ranar Lahadi, mutane suna rububin zuwa kasuwar, suna yin cinikin kayayyakin gargajiya da na wurin iri daban daban da kayayyakin da aka yi da hannu da kayayyakin kawo albarka da na masarufi da abinci da 'ya'yan itatuwa da kuma dabbobin gida iri daban daban a nan.

Da can ana bude babbar kasuwa ta Kashi a ran Lahadi, amma yanzu ana yin ciniki a wannan babbar kasuwa a ko wace rana. Amma idan kana son ka fahimci yadda babbar kasuwa ta Kashi take, ya fi kyau ka je wannan kasuwa a ran Lahadi.