Birnin da ake kira Tangshan cikin Sinanci yana arewacin kasar Sin. A ran 28 ga watan Yuli na shekarar 1976, wata mummunar girgizar kasa wanda ba a taba samun irinsa ba a cikin shekaru darurruwa da suka wuce a duniya, ta auku a birnin Tangshan mai nisan kilomita 150 kawai daga birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Karfinta ya ninka karfin atomic bomb har sau 400, irin wanda kasar Amurka ta taba amfani da shi a birnin Hiroshima na kasar Japan a lokacin yakin duniya na biyu. Nan take, wannan birni mai yawan mutane miliyan 1 ya ruguje gaba dayansa. Yawan mutane da suka rasa rayukansu ya kai dubu 240, yayin da wasu dubu 160 suka jikkata, ka zalika yawan kudi da aka yi hasara kai tsaye a fannin tattalin arziki ya wuce kudin Sin Yuan biliyan 10. Madam Wang Guiqin, malamar koyarwa wadda ta yi ritaya daga aikinta ta bayyana cewa, a wancan lokaci, birninmu ya zama wani birni ne da ba a zo a gani ba. Ta kara da cewa, "kafin girgizar kasar, iyalina muna kwana a kan bene na biyu na wani gida mai hawa biyu, amma duk gidanmu ya ruguje gaba daya a lokacin aukuwar girgizar kasar. Bayan da muka sauka a kasa, sai muka fita daga wata taga da ke arewancin gidan. A wannan lokaci, ana yayyafi, diyyata mai shekaru biyu kawai, don maganin ruwan sama, sai muka yi amfani da ganyaye wajen hada wata laima, muka tsunguna a gindinta."
Lalle, wahalhalu da bala'in ya haddasa ba za a iya mantawa da su ba. Yanzu idan wani ya sa kafa a kan wani babban titi mai suna "Xinhua" na birnin Tangshan, to, zai ga wasu kananan rusassun gine-gine a bakin titin wadanda kullum ke tunatar da mutane mummunar girgizar kasa da ta taba aukuwa a birnin.
A cikin shekaru 30 da suka wuce bayan aukuwar girgizar kasar, an sami ci gaba da sauri wajen bunkasuwar harkokin tattalin arziki a birnin Tangshan. Yawan kudin shiga da 'yan birnin ke samu ya yi ta karuwa da sauri. Matsakaicin yawan kudin shiga da ko wane dan birnin ya samu a shekarar bara ya karu da misalin sau 40 bisa na shekarar 1975 wato kafin aukuwar girgizar kasar. A gun wani bikin baje kolin motoci na kasa da kasa da aka shirya a birnin a kwanakin baya, an sayar da motoci 410 a cikin kwanaki biyar kawai. Daga binciken da aka yi, an ce, ko wadannen 'yan birnin biyar yana malakar mota daya. Madam Wang Meim wadda ke aiki a wani babban kamfanin gudanar da bikin baje koli ta birnin Tangshan ta bayyana cewa, "kamfaninmu ya shirya wannan bikin baje kolin motoci na kasa da kasa a birnin Tangshan. Manufarmu ita ce kara samun sabon ci gaba a gun irin wannan biki da mu kan shirya sau daya a ko wace shekara. Alal misali, yawan samfarorin motoci da muka shirya a gun bikin shekarar bara ya kai 70 kawai, amma ya karu zuwa 149 a shekarar nan. Daga cikinsu akwai motoci na yau da kullum, da kuma motoci masu tsananin tsada da aka shigo da su daga kasashen waje."
Ka zalika a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, birnin Tangshan ya yi ta samu ci gaba wajen jawo kudaden jari daga kasashen waje. Malam Chai Hongsheng, shugaban sashen kula da harkokin jari na hukumar kasuwanci ta birnin Tangshan ya bayyana cewa, "birnin Tangshan wani birni ne mai manyan masana'antu. Ayyukan narke karafa da na sarrafa kayayyakin gine-gine da na'urori ayyukan gargajiya ne ga birninmu. Mun jawo kudaden jari daga manyan kamfanonin kasa da kasa wajen gudanar da masana'antu ta hanyar zuba jari cikin hadin guiwa da sayar da hannun jari da sauransu. Birninmu ya kulla huldar hadin kai wajen zuba jari a tsakaninsa da manyan kamfanoni na kasashen Japan da Amurka da Faransa da Hong Kong da sauransu. Ta haka masana'antun narke karafa na birninmu ya kara daga matsayinta na kimiyya da kayayyakinta don yin takara a kasuwanni." (Halilu)
|