Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-11 18:48:47    
Kasar Sin alamar fata ce a idon Afirka, in ji jakadan Habasha da ke kasar Sin

cri

Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 50 da Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da kasashen Afirka suka kulla huldar jakadanci a tsakaninsu. A cikin shekarun nan 50 da suka wuce, ko da yake halin da kasashen duniya ke ciki na canjawa, amma huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Afirka ta jure wahaloli a fuskar lokaci, bangarorin 2 sun rika samun ci gaba a fannonin yin hadin gwiwar siyasa da tattalin arziki da al'adu da sauran fannoni lami lafiya, sun zama abin koyi ne wajen raya huldar da ke tsakanin kasashe masu tasowa. Jakadan kasar Habasha da ke kasar Sin Mr. Hailekiros Geseesee ya rubuta wani bayanin musamman kan huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Yanzu za mu dubu abubuwan da ke cikin bayaninsa.

A cikin shekaru gomai da suka gabata, har kullum bangarorin Sin da Afirka suna goyon baya da taimakawa juna da kuma kiyaye moriya iri daya na kasashe masu tasowa kan manyan al'amuran duniya da yankuna a cikin Majalisar Dinkin Duniya da sauran dandalin tattaunawa na duniya. Gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan yin hadin gwiwa da kasashen Afirka wajen tattalin arziki. Ta ba da taimakon kayayyaki da kudi da yawa ga kasashen Afirka, ta sa kaimi kan masana'antun kasarta da su zuba jari da kafa masana'antu a kasashen Afirka, ta kuma gaggauta yin hadin gwiwa tsakanin yankuna a fannonin ilmi da kiwon lafiya da yin mu'amalar al'adu, ta haka ta karfafa zumuncin da ke tsakaninta da kasashen Afirka. Har kullum kasar Sin tana aiwatar da manufofin jakadanci domin Afirka bisa ka'idojin girmamawar juna da yin zaman daidai wa daida, kasar Sin ba ta samar da ko wane sharadi ba a lokacin da take yin hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki da siyasa, musamman ma gwamnatin kasar Sin tana bai wa kasashen Afirka taimako ba tare da wani sharadi ba.

A cikin sabon karni na 21 da muke ciki, bangarorin Sin da Afirka suna fuskantar sabon halin da duniya ke ciki, suna bukatar tabbatar da sabbin manufofi don kyautata yin hadin kai da hadin gwiwa a tsakaninsu, da kuma raya huldar abokantaka da ke tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A cikin irin wannan hali ne, aka bude dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a watan Oktoba na shekarar 2000, wanda ya zama muhimmiyar alama ce a cikin tarihin dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka. Wannan muhimmin dandali ya tsara sabbin tsare-tsare kan raya huldar da ke tsakanin Sin da Afirka, muhimman takardu 2 wato 'sanarwar Beijing ta dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka' da 'tsarin ka'idoji na yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa' da aka zartas da su a gun wannan dandali na farko suna ba da jagora ga aikin kara yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.

Za a bude taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wato taron ministoci na karo na 3 a nan Beijing nan gaba ba da dadewa ba, wanda wani kasaitaccen biki ne a cikin tarihin dangantakar da ke tsakanin wadannan bangarori 2. A lokacin nan shugabannin kasashen Sin da Afirka za su taru a nan Beijing, za su yi tattaunawa kan zumunci da yin hadin gwiwa a tsakaninsu, za su kuma tsara shirye-shirye kan neman samun bunkasuwa da kuma samun makoma mai kyau. Ana sa ran cewa, za a tsara wasu takardu bisa muhimman tsare-tsare a gun wannan taro da za a yi, ta yadda za a kyautata yin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin Sin da Afirka.

A cikin karshen bayanin da ya rubuta, jakada Geseesee ya jaddada cewa, a idanun jama'ar kasashen Afirka, kasar Sin wata alama fata ce gare su. Za su yi koyi da nagartattun fasahohin da kasar Sin ta samu bisa halin da suke ciki. Kasashen Afirka suna bukatar kulla dangantakar abokantaka a tsakaninsu da kasar Sin daga duk fannoni, za su yi zaman daidai wa daida da moriyar juna da kuma yin hadin gwiwa da sahihanci, ta haka za su sami bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa.(Tasallah)