Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-11 18:11:32    
Kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha ta zama wani muhimmin batu da ake yin nazari a kai a kasar Sin

cri

A ran 18 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, an bude babban taro na farko na kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha a kasar Sin. Wakilinmu ya samu labari a gun taron, cewa a cikin hali mai tsanani da muhalli ke ciki yanzu, kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fahasa ya riga ya zama wani muhimmin batu da ake yin nazari a kai a kasar Sin a nan gaba. Shugaban babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin Zhou Shengxian ya bayyana a gun taron, cewa kasar Sin za ta kara zuba jari ga ayyukan kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha nan gaba, da soma aiki da wasu muhimman nazarin kimiyya da fasaha kan kiyaye muhalli a jere, da kuma karfafa zukatan kamfanoni kan nazarin fasahohi da kayayyakin kiyaye muhalli. To, yanzu ga cikakken bayani.

A cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, an samu bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin cikin sauri ne bisa abubuwan da aka sakadar kamar aiwatar da albarkatun kasa fiye da kima da kuma tsanantar muhallin halittu, kuma irin wannan salo na bunkasuwa ya riga ya zama wani muhimin sanadin kawo cikas ga ci gaban bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin.

Mataimakin shugaban ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Liu Yanhua ya bayyana a ran 18 ga wata a gun babban taron kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha na kasar Sin, cewa har zuwa yanzu ba a iya samun fasahohi masu amfani da kuma sakamako masu kyau daga kasashen waje kan warware matsalar muhalli ta kasar Sin ba, shi ya sa ba yadda za a yi sai kasar Sin ta nazari sabbin fasahohi don warware matsalar.

"matsalar muhalli ta kasar Sin ta fi ta kasashe masu ci gaba tsanani. A ko wace shekara, hasarar da aka samu sakamakon gurbacewa ta kai kashi biyar cikin dari bisa dukkan jimlar kudade da kasar Sin ta samu wajen samar da kayayyaki wato GDP. A cikin kauyukan kasar Sin, mutane kusan miliyan 360 suna shan ruwa maras tsabta. Fuskantar irin wannan matsalar gurbacewa mai tsanani, dole ne muka sarrafa fasahar shawo kan matsalar gurbatar da muhalli a wasu wurare da wasu koguna da kuma sauran muhimman batutuwan kimiyya, ta yadda za a tabbatar da samun dauwamammiyar ci gaba kan tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasa Sin. "

Bisa bayanin da aka yi, an ce, ban da matsalar gurbatar da muhalli, kasar Sin tana fuskantar matsalolin rashin yin amfani da albarkatun kasa da makamashi yadda ya kamata da tsanatar muhalli halittu da rashin albarkatun kasa da dai sauransu. Amma halin da kasar Sin ke ciki yanzu kan kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha bai iya dacewa da wannan halin muhalli mai tsanani da ake ciki ba, alal misali, fahasar shawo kan matsalar gurbacewa ba ta da kyau sosai, an rasa kididigar dudduba muhalli, kuma an rasa kudin nazarin kimiyya kan kiyaye muhalli sosai.

Sabo da haka, shugaban babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin Zhou Shengxian ya bayyana a gun taron, cewa domin kyautata hali maras kyau da ake ciki yanzu kan kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha, kasar Sin za ta kara zuba jari nan gaba, kuma za ta soma aiki da wasu muhimman nazarin kimiyya kan kiyaye muhalli a jere domin warware matsalar muhalli da take fuskantar yanzu.

Ban da wannan kuma Zhou Shengxian ya bayyana cewa, domin jawo hankulan mutane da za su zuba jari kan nazarin kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha, kasar Sin za ta karfafa zukatan kamfanonin gida da na waje wajen sa hannu a cikin ayyukan kago fasahohi da kayayyaki na kiyaye muhalli.

"Ya kamata a yarda da kamfanoni da suka sa hannu a cikin shirye-shiryen kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha da kuma muhimman ayyukan kiyaye muhalli, kuma a goyi bayan kamfanoni da su kafa hukumar nazari, da shugabanci kamfanoni da su yi nazari kan fasahohi da kayayyakin shawo kan abubuwan gurbacewa, da kuma karfafa zukatan kamfanonin kasashen waje da su kafa cibiyoyin nazarin fasahar kiyaye muhalli. "

Bugu da kari kuma kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen waje a fannin kiyaye muhalli ta hanyar kimiyya da fasaha, da koyi fasahohi da sakamako masu zamani daga kasashen waje kan kiyaye muhalli. Ban da wannan kuma za ta kara kago sabbin kayayyaki da fasahohi da kanta, ta yadda kasar Sin za ta sami fifiko tsakanin takarar da ake yi da kuma karfafa kwarjininta a duniya. (Kande Gao)