Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-11 18:04:08    
Kabilar Bulang

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kananan kabilun kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu gabatar muku da bayani kan kabilar Bulang ta kasar Sin, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani a karkashin lakabi haka: Ai Mang, mawaki na kabilar Wa ta kasar Sin. To, yanzu ga bayani.

An fi samun 'yan kabilar Bulang a shiyyar Xishuangbanna ta kabilar Dai mai cin gashin kai da ke jihar Yunnan ta kasar Sin. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin a karo na biyar da aka yi kidaya a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Bulang ya kai fiye da dubu 90. 'Yan kabilar suna yin amfani da harshen Bulang, wasu daga cikinsu sun iya magana da harshen Dai da Wa da kuma Han. Kabilar ba ta da harafinta, wasu 'yan kabilar suna iya gane harafin Han da Dai.

Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a cikin shekara ta 1949, a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, 'yan kabilar Bulang sun samu hakkin zaman daidai wa daida da kuma gudanar da harkoki da kansu. Gwamnatin kasar Sin ta yi gyare-gyaren gonaki a shiyyar kabilar Bulang bisa haliln da take ciki. A lokacin bazara na shekara ta 1953, an kammala yin gyare-gyaren gonaki a wurare masu gwargwadon ci gaba. A wurare marasa ci gaba, a lokacin kaka na shekara ta 1956, an dauki matakai kan yin gyare-gyaren gonaki lami lafiya. Haka kuma a cikin sauran wurare na zamantakewar al'umma mai duhun kai, gwamnatin kasar ta ba su taimako wajen samar da albarkatun gona domin kawar da sauran tsari marasa ci gaba. Sabo da taimakon da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da sauran kananan kabilun Sin suka bayar, sha'anin noma na kabilar Bulang ya samu bunkasuwa cikin sauri. Ban da wannan kuma an raya cinikayya sosai, an kafa kamfanonin cinikayya na kabilar a wurera daban daban. Bugu da kari kuma sha'anin ilmi da kiwon lafiya na shiyyar kabilar Bulang ya samu ci gaba, an kafa firamare da asibitoci a shiyyar, ta haka an shawo kan ciwon malariya da ya taba yaduwa sosai a shiyyar, kuma an kyautata lafiyar 'yan kabilar kwarai da gaske.

Kabilar Bulang tana da al'adun gargajiya iri daban daban, kuma ana iya samun adabin gargajiya na baka na kabilar da yawa. Wakoki da rawa na kabilar Dai sun taka muhimmiyar rawa ga kabilar Bulang sosai. Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan Ai Mang, wani mawaki na kabilar Wa ta kasar Sin.