Bisa sabuwar kididdigar da ma'aikatar kiwon lafiya na kasar Kwadivwa ta bayar a ran 9 ga wata, an ce, ya zuwa ran 8 ga wata, mutanen kasar fiye da 1500 sun sha dafi sakamakon kayayyakin guba da aka zubar a birnin Abidjan.
Yanzu, gwamnatin Kwadivwa ta riga ta dauki jerin matakai cikin gaggawa domin hana tsananta halin da ake ciki. Wato, mutane wadanda suka sha dafi za su iya samun jiyya ba tare da biyan kudi ba, da ware wurare masu kazamtarwa kuma da kiyaye asalin ruwan sha da dai sauransu. A sa'i daya kuma, gwamnatin ta fara binciken al'amarin nan. (Sanusi Chen)
|