Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-08 16:53:19    
Dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasar Sin da Afrika zai gaggauta yunkurin kulla sabuwar dangantakar abokantaka ta muhimmman tsare-tsare dake tsakaninsu

cri

Za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da kuma taro na 3 na matakin mukamin minista daga ran 3 zuwa ran 5 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki a nan Beijing. Kwararrun da abun ya shafa na kasar Sin sun yi hasashen, cewa kiran taron zai ingiza kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da kuma taka muhimmiyar rawa wajen kara kyautata irin wannan hulda a nan gaba da kuma gaggauta yunkurin kulla sabuwar dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare.

Madam He Wenping, manazarciyar ofishin nazarin harkokin Yammacin Asiya da na Afrika ta kolejin kimiyya da zamantakewar al'umma na kasar Sin ta fadi, cewa za a gudanar da wannan taron koli ne daidai a zagayowar ranar cika shekaru 50 da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. 'Lallai wannan wani gagarumin sha'ani ne na tarihin dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kuma wani babban sha'ani ne na tarihin harkokin waje na kasar Sin'.

Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, yawan shugabannin kasashen Afrika wadanda za su zo nan kasar Sin domin halartar wannan taron koli ya kai kusan 40, wadanda ko shakka babu za su taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

Ban da wannan kuma, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mr. Qingang ya bayyana, cewa babban taken taron kolin shi ne ' Zumunci, da zaman lafiya, da hadin gwiwa da kuma yalwatuwa'. A gun taron kolin, shugabannin kasar Sin da na Afrika za su fi ba da muhimmanci kan wannan babban take don waiwayen tarihin kyakkyawan hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a cikin shekaru 50 da suka shige da kuma nasarorin da aka samu tun bayan da aka aka kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afrika, sa'annan za su tsara shirin kara hadin kansu a nan gaba da kuma yin musayar ra'ayoyi kan wassu muhimman maganganun kasashen duniya.

Jama'a masu saurare, kuna sane da, cewa a farkon wannan shekara, a karo na farko ne gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da ' Takarda kan manufar kasar Sin game da harkokin Afrika', wacce ta bayyana babban burin kasar Sin na kulla sabuwar dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare tare da kasashen Afrika bisa matsayin daidaici da amince wa juna a fannin siyasa, da samun moriyar juna a fannin tattalin arziki da kuma yin ma'amala da juna a fannin al'adu. Ban da wannan kuma, shugaba Hu Jintao da firaminista Wen Jiabao na kasar Sin sun kai ziyarar gani da ido daya bayan daya zuwa kasashe 10 na Afrika a watan Afrilu da watan Yuni na wannan shekara.

Shahararren dan diplomasiyya kuma shugaban hukumar nazarin harkokin Afrika ta kasar Sin Mr. An Yongyu ya furta, cewa a cikin shekara daya, shugaban kasa da kuma firaministan kasar sun kai ziyara a Nahiyar Afrika a sa'I daya, wannan dai ba safai akan ga irinsa a cikin tarihin harkokin waje na kasar Sin kuma ya shaida, cewa kasar Sin na mai da hankali sosai kan harkokin Afrika. Mr. An Yongyu ya kara da, cewa Nahiyar Afrika, babbar nahiya ce dake kasancewar kasashe masu tasowa mafiya yawa; kuma kasar Sin, wata kasa ce mai tasowa kuma mafi girma a duniya. Inganta dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, wani irin zabe ne na muhimman tsare-tsare da kasar Sin take yi cikin dogon lokaci.

Kazalika, daraktan ofishin nazarin harkokin Afrika na hukumar nazarin huldar kasa da kasa ta zamanin yanzu ta kasar Sin Mr; Xu Weizhong ya bayyana ra'ayinsa, cewa kasashe masu hannu da shuni na yamma sukan kulla hulda maras daidaici tsakaninsu da kasashen Afrika, wato ke nan sukan aiwatar da manufofinsu ala-tilas yayin da suke yarje wa kasashen Afrika gudummowa; Amma kasar Sin ta haka take yi ba, wato ke nan ta ba da shawarar kafa dangantakar hadin gwiwa bisa matsayin yin shawarwari cikin halin daidaici da kuma samun moriyar juna.

An labarta, cewa a duk tsawon lokacin taron kolin, za a shirya taron fadin albarkacin bakinsu tsakanin shugabannin kasar Sin da na kasashen Afrika da kuma manyan jami'ai daga masana'antu da sassan kasuwanci da kuma babban taro na 2 na masu masana'antun kasar Sin da na Afrika. ( Sani Wang )