sakamakon bala'in da suka obkawa kasar Sin a shekarar da muke ciki, shi ya sa gwamnatin kasar Sin ta ware kudi yuan miliyan 220 domin gudanar da ayyukan sake gina wuraren mahaukaciyar guguwa da bala'in fari na kasar Sin.
Bisa labarin da muka samu, an ce, ana mai da hankali a kan sake gina dakunan makarantun firamare da na sakandare, da asibitoci a garuruwa da kauyuka, da samar da ruwan sha a garuruwa da kauyuka, da kuma kananan kayayyakin ban ruwa da dai sauransu, ta yadda za a taimakawa yankunan da suka sha bala'in wajen kyautata harkokin zaman rayuwa da ayyukan samar da amfanin gona, da kuma sake mai da oda yadda ya kamata.(Kande Gao)
|