A ran 7 ga wata da dare, a birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon, firayim ministan kasar Lebanon Fouad Siniora ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne kasar Isra'ila za ta janye datsen tasoshin jiragen ruwa na kasar Lebanon a ran 8 ga wata.
Mr. Siniora ya yi bayani a gun wani taron manema labarai da aka shirya bayan da Isra'ila ta janye datsen filayen jiragen sama na Lebanon a ranar, cewa MDD ta gamu da wata karamar matsala kan maganar janye datsen tasoshin jiragen ruwa da Isra'ila za ta yi wa Lebanon. Amma za a warware matsalar a ran 8 ga wata da safe.
Bisa wani labarin da muka samu, an ce, bangaren Isra'ila yana fatan sojojin jiragen ruwa na kiyaye zaman lafiya na MDD za su shiga tasohin Lebanon tun da wuri, ta yadda Isra'ila za ta iya janye datsen tasoshin jiragen ruwa na Lebanon. Amma MDD ba ta amince da wannan shawara ba sabo da ana kasancewar sabani kan wa zai kula da harkokin dudduba hadin ruwan teku na Lebanon. Gwamnatin kasar Lebanon tana fatan MDD za ta taimake ta wajen aikin. Kuma kafofin watsa labarai na wurin sun kiyasta cewa, da farko sojojin jiragen ruwa na kasashen Italiya da Faransa za su dauki nauyin aikin bisa wuyansu, daga baya kuma za su mika aikin ga kasar Jamus.(Kande Gao)
|