A ran 7 ga wata a birnin Copenhagen, babban birnin kasar Danmark babban wakilin kungiyar tarayyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaron kai Javier Solana ya bayyana cewa, a ran 9 ga wata, zai yi shawarwari da Ali Larijani, wakili na farko na kasar Iran a kan yin shawarwari dangane da batun nukiliya.
A ranar, Mr Solana ya ce, zai yi shawarwari da bangaren kasar Iran a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran, amma bai tabo magana a kan wurin da za a yi shawarwari ba. Bisa shirin da aka yi a da, ya kamata Mr Solana da Mr Larijani su yi shawarwari a ranar 6 ga wata a birnin Vienna domin karin haske a kan amsa da kasar Iran ta bayar game da shirin da kasashe shida suka gabatar, amma aka jinkirtar wannan lokaci.(Danladi)
|