Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-06 21:40:13    
Kungfu na Shaolin

cri
Kwanan nan, mai sauraronmu daga birnin Zaria na jihar Kaduna ta kasar Nijeriya, Sarki Bambale ya aiko mana wasika, inda ya yi mana tambaya cewa, shin mene ne asalin wasan da ake yi na Kungfu fighting ko Shaolin? Ban da wannan, malam Hamza M Djibo daga jamhuriyar Nijer ya aiko mana wasikar Email cewa, don Allah, ina so ku binciko mini tarihin Jet Lee, kuma fim nawa ya yi zuwa yanzu. Mun san aminanmu masu yawa na kasashen waje suna matukar sha'awar wasan karate na kasar Sin da kuma fina-finan kasar Sin na game da wasan Kungfu, kuma a ganin mutanen duniya, wasan Kungfu wata muhimmiyar alama ce ta al'adun kasar Sin. To, bari mu yi muku bayani a kan wasan Kungfu na Shaolin na kasar Sin da kuma tauraron fim din nan na wasan Kungfu wanda ake san shi da suna Jet Lee.

Wasan Kungfu na Shaolin wani rukuni ne na shahararrun wasannin karate na kasar Sin, yana da dogon tarihi, kuma yana bayar da babban tasiri.

Wasan karate na Shaolin ya samo asalinsa ne daga wurin ibada mai suna Shaolin, sabo da haka kuma, ake kiransa 'wasan Kungfu na Shaolin'.

Wurin ibada na Shaolin yana dutsen Songshan da ke gundumar Dengfeng ta lardin Henan na kasar Sin, kuma an gina shi ne a shekara ta 495, don zaunad da Batuo, wato wani malamin addinin Buddah na kasar Indiya wanda ya zo dutsen Songshan ne domin yada addinin Buddah.

Bayan da malami Batuo ya kama ragamar jagorancin wurin Ibada na Shaolin, sai masana masu yawa suka zo wurin, suna biye da shi. Sabo da haka, masu wasan karate da yawa sun fara yin hidimomi daban daban a wurin. Ban da wannan, a lokacin da malami Batuo ke shugabantar wurin Ibada na Shaolin, akwai wasu matasa da suka iya wasan Kungfu ko sauran fasahohi wadanda aka yi musu aski, don su zama sufayen addinin Buddah a wurin Ibada na Shaolin. Malami Batuo ya ba da babban taimako a wajen gina wurin Ibada na Shaolin da kuma yada addinin Buddah.

An ce, a shekara ta 527, Damo, wani babban malamin addinin Buddah na kasar Indiya, shi ma ya zo wurin Ibada na Shaolin don yada addinin Buddah. A lokacin, yayin da Damo ke yin zaman natsuwa don zurfafa tunaninsa dangane da addinin Buddah, ya kan gaji. Ga shi kuma, zama cikin daji, ya zama dole a magance harin naman daji da sanyi ko zafi mai tsanani. A sa'i daya kuma, yayin da yake yada addinin Buddah, ya gano cewa, mabiyansa su kan rasa kuzari a yayin da suke zaman natsuwa cikin dogon lokaci. Domin kawar da gajiya da maganin naman daji da motsa jiki da kuma kare wurin ibada din nan na Shaolin, malami Damo ya kwaikwayi wasannin motsa jiki iri iri da fararen hula na kasar Sin su kan yi a da, kuma ya gyara su ya koyar da su ga sauran sufaye, wato su ne suka zama asalin wasan dambe na Shaolin ke nan. Daga baya, sufaye na zamani daban daban sun yi ta inganta wasan, har ma ya zama wani tsari da ke da wasannin dambe sama da 100, wanda ake kira wasan dambe na Shaolin.

Bayan haka, an kuma yi ta gayyatar gwanayen wasan Kungfu da su zo wurin Ibada na Shaolin don su koyar da wasanni iri iri, ta yadda za a bunkasa wasan Kungfu na Shaolin. Sabo da haka, wurin Ibada na Shaolin ya zama wani wuri da kwararrun wasan Kungfu ke haduwa. Bayan da wasan Kungfu na Shaolin ya dauko kyawawan wasanni na rukunoni daban daban, sannu a hankali ne sai ya bunkasa har ya zama wani rukuni na wasan Kungfu da ke da wasanni iri iri. Daga baya, sufayen wurin Ibada na Shaolin na zamani daban daban sun kuma yi ta bunkasa wasan har sun sa wasan Shaolin ya shahara a duk duniya.

An haifi Jet Lee ne a shekara ta 1963 a birnin Beijing na kasar Sin. A lokacin da yake makarantar firamare, wani malamin wasan Kungfu na birnin Beijing ya gano gwanintarsa a wajen wasan Kungfu, yayin da Jet Lee ke yin wani kwas na koyon wasan karate. Sabo da haka, Jet Lee ya kama hanyar yin wasan Kungfu. Domin gwanintarsa, a lokacin da shekarunsa ya kai 11, a karo na farko ne ya zama zakara a gasar wasan karate. Daga bisani a shekaru 5 a jere, ya sami lambobin zinari kan duk fannoni na wasan karate. Sabo da kyawawan ayyukansa a wajen wasan Kungfu, shi ya sa Jet Lee ya jawo hankalin kamfanin fina-finai na Yindu na Hongkong, har ma ya zamo wani tauraron fim da ke karkashin tutar kamfanin nan. Daga nan kuma, ya kama aikinsa a fagen fina-finai.

A farkon shekarun 1980, Jet Lee wanda a lokacin shekarunsa bai kai 20 ba, ya yi suna a gida da kuma kasashen ketare sakamakon wani fim dinsa na farko mai suna 'wurin ibada na Shaolin', har ma Jet Lee ya sake jawo hankulan duniya a kan wasan karate bayan Bruce Lee. Daga baya kuma, Jet Lee ya hada gwiwarsa da wani mashahurin darektan fim mai suna Xu Ke, sun yi fina-finai da dama dangane da wasan Kungfu, wadanda suka sami nasarori da dama. Bayan shekara ta 1997, Jet Lee ya je Hollywood don bunkasa sha'aninsa a dandalin fina-finai na duniya, inda ya fitar da fina-finai da dama wadanda suka sami karbuwa sosai, ciki har da 'Lethal Weapon 4'.

Ko da yake Jet Lee ya je Hollywood, amma a cewarsa, yana ci gaba da rike da halaye irin na mutanen gabashin duniya. Ya ce, 'yanzu na gaya maka me zan yi, amma watakila bayan shekaru 3, zan canja, sabo da muhalli ya canja, shi ya sa ni ma zan canja. Amma akwai wani abin da ba zai canja ba, wato ni Basine na gargajiya ne har abada.'

A cikin shekaru 20 da suka wuce tun bayan da Jet Lee ya kama hanyar yin fina-finai, ya nuna wa duniya kyawawan al'adun wasan Kungfu na kasar Sin. Jet Lee ya kuma zama wani babban malamin wasan karate bayan Bruce Lee, kuma ya zama wata alama daban ta wasan karate na kasar Sin. (Lubabatu)