Ko da yake Wu Cheng'en ya rubuta littafin "Pilgrimage to the west" a karshen rayuwarsa a duniya, amma ya yi shirin rubutun nan ne a duk rayuwarsa. A kokacin da ya ke karami, ya kan kai ziyara a haikali na zamanin da a karkarar da ke dab da birnin Huai'an tare da mahaifinsa, inda mahaifinsa ya bayyana masa tsatsuniyoyi masu ban sha'awa da suke da nasaba da wurin. A wancan zamani, yana da sha'awar saurarar abubuwan mamaki, bayan da ya cika shekaru 30 da haihuwa, ya tanadi tatsuniyoyi da yawa a cikin zuciyarsa , sai ya yi shirin rubuta wani littafi, wajen lokacin da ya cika shekaru 50 da haihuwa, ya kammala rubuta rabin littafin, amma ya dakatar da rubutun nan har cikin wasu shekaru , har zuwa karshen rayuwarsa, ya kammala rubutun nan.
Littafin yana kunshe da tatsuniyoyi fiye da 100, wadanda kowanensu na iya zama shi kadai kawai, kuma yake da nasaba da sauransu. A cikin kagaggen labarai da ya wallafa, da akwai aljanna da iskoki da sauran irin makamatansu, kowanensu ya iya wakiltar adalci ko marasa adalci. A cikin littafin nan, mawallafin ya samar wa masu karantawa wata duniyar tatsuniya mai ban mamaki sosai. A cikin duniyar kuma, da akwai almomin mutane a duniyar yau a ko'ina, wato alamomin sarakunan da ba su iya bambanta masu kirki da wawa , fadar kasa shi ne tamkar yadda daulolin mulkin gargajiya suke yi, a ciki, ake cin hanci da rashawa da keta dokokin shari'a da dai sauran miyagun ayyuka, aljanna da iskoki suna cinye mutane da kuma son mata da dukiyoyi, kai babu miyagun ayyukan da ba su yi ba. Amma Sun Wukong wato sarkin biri da mawallafi Wu Cheng'en ya wallafa yana da karfi sosai, ya fattattaka dukan aljanna da iskoki, a wajen sarkin birin nan, Wu Cheng'en ya bayyana dukan fatansa na kawar da miyagun ayyukan da aka yi a zamantakewar al'umma.(Halima) 1 2 3
|