Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-06 09:29:08    
Kungiyar wasan kwallon kwando ta maza ta kasar Sin tana sanya kokari domin taron wasannin Olimpic na shekara ta 2008

cri

Kungiyar wasan kwallon kwando ta maza ta kasar Sin tana sanya matukar kokari domin taron wasannin Olimpic na shekara ta 2008. Daga ran 19 ga watan Agusta zuwa ran 3 ga wannan wata,a kasar Japan,an yi gasar cin kofi ta wasan kwallon kwando ta maza ta duniya.A ran 27 ga watan jiya,a cikin gasar da aka yi tsakanin kungiyoyi sha shida,wato ko wadannen kungiyoyi biyu sun yi gasa bisa ka`idar da aka tsara,kungiyar maza ta kasar Sin ta kasa ci wato ba ta lashe kungiya ta kasar Greece wadda ita ce kungiya ta zakara a shiyyar Turai ba,makinsu shi ne 64 na kasar Sin bisa 95 na kasar Greece,saboda haka kungiyar kasar Sin ba ta shiga kungiyoyi mafiya karfi guda 8 ba.Amma duk da haka,kokarin da `yan wasan kasar Sin suka yi a cikin wannan gasa ya sami yabo sosai daga duk fannoni,ana fatan kungiyar wasan kwallon kwando ta maza ta kasar Sin za ta sami babban ci gaba a gun taron wasannin Olimpic da za a yi a shekara ta 2008 a birnin Beijing.Yanzu ga cikakken bayani kan wannan.

An yi gasar cin kofin wasan kwallon kwando na maza na wannan shekara a birane biyar na kasar Japan,gaba daya yawan kungiyoyin da suka shiga wannan gasa ya kai 24 wadanda ke kunshe da kungiyar kasar Sin da ta kasar Amurka da ta Argentina da sauransu.An fara gasar ne daga ran 19 ga watan jiya,a ran 3 ga wannan wata kuwa zakara ta fito.Bisa matsayinta na zakara ta shiyyar Asiya,kungiyar kasar Sin tana cikin rukunin D tare da sauran kungiyoyi biyar,kuma a cikin gasar karamar kungiya,ta taba zama daya daga cikin kungiyoyi mafiya karfi guda 16,wato wannan ne sakamako mafi kyau da kungiyar maza ta kasar Sin ta samu a cikin gasar cin kofi ta wasan kwallon kwando ta maza ta duniya tun bayan shekara ta 1994.

A cikin karo na karshe na gasar karamar kungiya,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Slovenia da maki 78 bisa 77.Bayan wannan,`dan wasa wanda ya jefa kwallo ta karshe cikin kwando Wang Shipeng ya ce: `Ina ganin cewa,imani yana da muhimmanci sosai gare mu,idan mun lashe wasu kungiyoyi masu karfi,zai taimaka mana sosai,kuma na hakake cewa ko shakka babu kungiyar kasar Sin za ta kara karfi,kuma za ta sami sakamako mai kyau a gun taron wasannin Olimpic na shekara ta 2008.`

Game da shahararren `dan wasan kasar Sin Yao Ming wanda ya fi kwarewa wajen wasan,babban malamin koyarwa na kungiyar kasar Amurka Mike Krzyzewski ya yi sharhi cewa:`Yao Ming yana da muhimmanci sosai ga kungiyar kasar Sin,kuma yana da karfin zuciya,ana iya cewa Yao Ming shi ne shugaban kungiyar `yan wasa mai kyau,ya sa sauran `yan wasa su cike da imani,na san Yao Ming ya warke daga ciwon kafa ba da dadewa ba,amma ya yi kokari fiye da kimanmu,ina jin dadinsa kwarai da gaske.`

Yanzu,kodayake kungiyar wasan kwallon kwando ta maza ta kasar Sin ta riga ta shiga jerin kungiyoyi mafiya karfi guda sha shida a duniya,amma dole ne ta ci gaba da sanya matukar kokari idan tana so ta yi takara da kungiyoyi masu karfi na duniya.Bayan gasar da aka yi tsakanin kungiyar kasar Sin da ta kasar Greece,mataimakin shugaban kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin Hu Jiashi ya bayyana cewa,yayin da ake yin gasar tsakanin kungiyar kasar Sin da kungiyoyi masu karfi na duniya,kungiyar kasar Sin ta gamu da matsaloli da yawa da take fuskanta,dole ne `yan wasa na kasar Sin su mai da hankali kan wannan,haka kuma za ta sami ci gaba,daga baya kuma za ta sami babban sakamako mai faranta ran mutane a gun taron wasannin Olimpic na shekara ta 2008.Ya ce: `Daga gasar da ta wuce,da farko dai,ana iya ganin cewa,`yan wasan kasar Sin ba su iya yin kokari tare kamar yadda ya kamata ba,dalilin da ya sa haka shi ne domin raunin da suka ji;ban da wannan kuma,jikin `yan wasan kasar Sin ba su da karfi sosai ba,kuma karfin yin gaba nasu shi ma ba shi da kyau sosai;bisa na uku kuwa,`yan wasanmu ba su iya yin wasan kwallon kwando cikin sauri kamar yadda sauran kungiyoyi masu karfi suke yi ba.`

Babban malamin koyarwa na kungiyar kasar Sin Jonas Kazlauskas ya dauka cewa,yanzu kodayake Yao Ming yana cikin kungiyar wasan kwallon kwando ta maza ta kasar Sin,amma idan kungiyar kasar Sin tana so ta ci gaba da samun babban sakamako a gun taron wasannin Olimpic na Beijing,dole ne ta kara karfinta daga duk fannoni.To,a halin da ake ciki yanzu,dabara mafi sauki ita ce a tura `yan wasa zuwa kasashen waje domin su tattara fasahohi da sakamakon gasa iri ta matsayin koli,musamman a tura `yan wasa zuwa kasashen Turai domin su shiga hadaddiyar gasar da aka shirya a can.(Jamila)