1)A ran 31 ga watan jiya a birnin Beijing,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing da gwamnatin yankin musamman ta Hongkong sun sa hannu kan wata takarda kan aikin shirya gasar wasan tseren doki a gun taron wasannin Olimpic na shekara ta 2008,wannan takarda ta tanadi ka`idoji masu tushe wajen daidaita huldar tsakanin bangarori daban daban yayin da ake shirya gasar.Wannan ya alamanta cewa,aikin shirya gasar wasan tseren doki na taron wasannin Olimpic ya riga ya shiga wani sabon mataki.Kafin wannan kuma,an riga an canja wurin yin gasar wato za a yi gasar wasan tseren doki na taron wasannin Olimpic na Beijing a Hongkong na kasar Sin.
2)A ran 2 ga wata,shugaban kwamitin wasannin Olimpic na duniya Jacques Rogge ya karbi ziyarar da manema labaru suka yi masa a birnin Athens na kasar Greece inda ya darajanta aikin shirya taron wasannin Olimpic da birnin Beijing ke yi sosai,ya ce,`Birnin Beijing zai ci nasara,mun ga Beijing ya riga ya yi manyan sauye-sauye,ko shakka babu abokana na kasar Sin za su gudanar da taron wasannin Olimpic kamar yadda ya kamata.`
3)A ran 3 ga wata,a birnin Moscow na kasar Rasha,an kawo karshen zama na 3 na gasar cin kofin wasan kwallon kafa na mata na duniya `yan kasa da shekaru 20,a cikin gasa ta karon karshe,kungiyar kasar Korea ta arewa ta lashe kungiya ta kasar Sin da ci biyar da ba ko daya,wato kungiya ta kasar Sin ta zama lambatu.
4)A ran 3 ga wata da dare,a birnin Saitama na kasar Japan,an kammala gasar cin kofin wasan kwallon kwando na maza na duniya na shekara ta 2006.Kungiyar kasar Spain ta lashe kungiya ta kasar Greece da maki 70 bisa 47,wannan ne karo na farko a tarihi da ta zama zakara ta gasar cin kofin wasan kwallon kwando na maza na duniya.
5)A ran 30 ga watan jiya,a birnin Beijing,an kafa kwamitin shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa na mata ta shekara ta 2007,wannan ya alamanta cewa,ana gudanar da aikin shirya wannan gasa mai matsayin koli wadda za a yi a birnin Tianjing da na Shanghai da na Wuhan da na Hangzhou da na Chengdu daga ran 10 zuwa ran 31 ga watan Satumba na shekara mai zuwa yadda ya kamata kuma lami lafiya.(Jamila)
|