Gidan ibada mai suna Chongsheng da ke gunduma ta kabilar Bai ta Dali mai tafiyar da harkokinta da kanta a lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, wanda shekarunsa ya kai fiye da dubu 1. A kwanan baya, mahukuntan wurin sun yi kwaskwarima kan wannan tsohon gidan ibada, sun kuma shirya kasaitaccen bikin kaddamar da soma aiki da mutum-mutumin Buddha. Bayan kwaskwarimar da aka yi masa, wannan gidan ibada ya nuna halin musamman na sarauta da na kabilu. A cikin shirinmu na yau, za mu ja gorancinku zuwa ziyarar gidan ibada mai suna Chongsheng.
Manyan sufaye 108 da suka zo daga babban yankin kasar Sin da kasashen kudu maso gabashin Asiya da na kudancin Asiya sun shugabanci kasaitaccen bikin kaddamar da soma aiki da mutm-mutumin Buddha cikin hadin gwiwa. An shimfida kafet mai launin ja a kan hanyar da ke tsakanin babbar kofar gidan ibada zuwa babban daki mai suna Da Xiong Bao Dian, sa'an nan mabiyan addinin Buddha sun yi maraba da masu yawo shakatawa da masu halartar wannan biki a gefuna 2.
Wani suna daban na gidan ibada na Chongsheng shi ne Santa, yana dogara wani babban tsauni, inda akwai kankara mai laushi a kansa, kuma yana fuskantar tekun Erhai, inda ruwa mai tsabta sosai. Saboda girgizar kasa da yake-yake, yanzu hasumiyoyi 3 ne kawai suke ci gaba da tsayawa a cikin wannan gidan ibada. Bayan da aka yi masa kwaskwarima, ba ma gine-gine suna cin gaba da nuna salo na da kawai ba, har ma an mai da kayayyakin gargajiya a wurarensu.
Mr. Wang Hai da matarsa sun zo nan don kallon wannan gaggarumin biki daga birnin Kunming, babban birnin lardin Yunnan. Sun darajanta gidan ibada na Chongsheng na yanzu. Mr. Wang ya ce,
'a zahiri, wannan gidan ibada ya nuna halin musamman na sarauta, yana da girma. Ina jin dadi sosai saboda ziyararsa, ya zama na farko a duk kasarmu. Mun taba ziyarar wurare masu yawa, a ganina ba za a iya kwatanta su da wannan gidan ibada a fannin muhalli ba.'
A cikin tarihinsa, gidan ibada na Chongsheng cibiya ce wajen tafiyar da harkokin addinin Buddha a kudancin kasar Sin har ma a yankin kudu maso gabashin Asiya, mabiyan addinin Buddha na kudu maso gabashin Asiya sun mayar da shi a matsayin babban birni ne na addinin Buddha. A gun bikin kaddamar da soma aiki da mutum-mutumin Buddha da aka yi a nan, manyan sufaye 108 da suka zo daga kasashen Sin da Korea ta Kudu da Singapore da Indonesia da sauran kasashe sun karanta littattafan addinin Buddha, da shugabancin harkoki iri daban daban na addinin Buddha, sun kaddamar da soma aiki da mutum-mutumin Buddha.
Madam Li Ying, wata mabiyiyyar addinin Buddha ce da ke yin imani ga addinin Buddha, shekarunta ya kai 65 da haihuwa. Ta jiku da fadin cewa, ta ji alfahari sosai saboda halartar wannan muhimmin biki da kuma ganin manyan sufaye na gida da waje a gun wannan biki. Ta ce, 'na ji alhafari sosai saboda ganin manyan sufaye na wurare daban daban na kasar da kuma shugaban hadadiyyar kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin. Ina jin dadi kwarai saboda halartar wannan muhimmin biki tare da manyan sufaye masu yawan haka, kuma na dauki hotuna tare da su.'
Masu yawon shakatawa sun rika shiga cikin gidan ibada na Chongsheng, suna yin amfani da yarukan wurare daban daban, suna tsayawa a cikin wannan gidan ibada mai kyan gani, suna jin dadin ganin wurare masu ni'ima a kewayensu. Wakilinmu ya yi hira da Mr. Mike Jackson, dan kasar Cyprus. Mr. Jackson ya yi bayyani kan ziyararsa a wannan gidan ibada, ya ce, 'wannan gidan ibada yana da kyaun gani kwarai, haka kuma yana da girma, na ji mamaki sosai. Wannan karo ne na farko da na ziyarci wannan birni, amma na ziyarci kasar Sin har sau 5. Matata ta taba ambata wannan gidan ibada, ita Basinniya. Wannan gidan ibada ya faranta mini rai.'
Ya kara da cewa, yin kwaskwarima da sake gina gidan ibada na Chongsheng alheri ne da gwamnatin kasar Sin ta kawo wa mabiyan addinin Buddha. Ya yi imani cewa, saboda shirya bikin kaddamar da soma aiki da mutum-mutumin Buddha da aka yi, gidan ibada na Chongsheng zai sake ba da haske.(Tasallah)
|