Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-05 20:35:57    
Masallacin Ai Ti Ga Er

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan masallacin Ai Ti Ga Er da ke cikin yankin Kashi na jihar Xinjiang mai tafiyar da harkokinta da kanta ta kasar Sin, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, ziyarar gidan ibada mai suna Chong Sheng.

Masallacin Ai Ti Ga Er masallaci ne mafi girma a duk kasar Sin, kuma shi ne alama na yankin Kashi. An gina dakin yin salla da burki, katangarsa rawaya ne wadda aka yi masa ado da fale-falen burki masu launin kore da shudi, shi ya sa ya jawo hankulan mutane sosai.

An gina wani karamin masallaci a nan a shekarar 1442 don tunawa da dangogi da abokai wadanda suka rigamu gidan gaskiya. A shekarar 1538, an fadada gina wannan masallaci da ya zama babban masallaci ga Musulmai wajen yin Salla tare. Daga baya kuma, saboda sha yin kwaskwarima da fadada, masallacin Ai Ti Ga Er ya yi girma kamar yadda yake a yanzu.

Babbar hasumiyar kofa tana tsaye a gaban wannan masallaci, an kera kofofi 2 da tagulla. Babban gini na masallacin Ai Ti Ga Er shi ne dakin yin salla, wanda zurfinsa ya kai mita 20, fadinsa ya kai mita 140, an raba shi zuwa kashi 2, wato na gida da na waje. Ginshikan katako 140 suna tallafe da babban dakin, kuma akwai isasshen haske a nan. Saboda Makka tana yammacin kasar Sin, shi ya sa Musulmai ke fuskantar yamma yayin da suke salla, an gina kofar dakin yin salla zuwa gabas.

Dukan musulmi da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin suna taruwa su yi salla a masallacin Ai Ti Ga Er. Musulmi dubu 2 zuwa dubu 3 ne ke yin salla a nan a ko wace rana, a ran Jumma'a da yamma, dukan musulmi maza sun je nan don yin sallar Jumma'a, a lokacin nan, yawan musulmin da ke cikin wannan masallaci ya kai dubu 6 zuwa dubu 7.

A lokacin babbar Salla, a cikin masallacin AI Ti Ga Er, yawan musulmi daga wurare daban daban na jihar Xinjiang da wadanda ke zama a wurin da suka yi salla ya kai dubu 20 zuwa dubu 30. Bayan da suka yi salla, mutane masu yawa sun taya juna murna tare, su yi kide-kide masu dadin ji. Musulmi maza suna rawa bisa kide-kide a duk dare.(Tasallah)