Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-05 20:17:31    
Kasashen Larabawa sun tsai da kudurin kai agaji tare ga kasar Lebanon don farfado da kasar

cri

Wakilin Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ruwaito mana labari cewa , a ran 4 ga watan nan a birnin Alkahira Kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta yi taro na 78 . Kasashe mambobin Kungiyar sun tsai da kuduri cewa , a watan Okotoba za a yi taron musamman a birnin Berut , hedkwatar kasar Lebanon don tattauna matsalar yadda za a goyi bayan aikin farfado da kasar Lebanon .

A ran 25 ga watan Yuli , Sojojin Kasar Isra'ila sun jefa bom a Garin Khiyam dake kudancin kasar Lebanon inda Majalisar Dinkin Duniya ta girke sojojinta . Wannan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 4 na Majalisar Dinkin Duniya ciki har da wani sojan Kasar Sin .

A wannan rana da dare Kamfanin MENA wato kamfanin dillancin labaru na kasar Masar ya tsamo labarin da jam'iyyar Hezbollah ta Lebanon ta bayar cewa , tun daga ran 25 sojojin kasar Isra'ila sun kai farmaki ga Garin Khiyam fiye da sau 100 .

Kofi Annan , Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da sanarwa cewa , ya yi mamaki kwarai da gaske ga kasar Isra'ila kuma ya nemi sojojin kasar da su daina kai irin wannan farmaki . Masu binciken lamarin duniya sun bayyana cewa , kamar yadda Mr. Annan , babban sakataren MDD ya ce , Cibiyar binciken sojojin Majalisar Dinkin Duniya wadda ta gamu da farmakin da Isra'ila ta kai mata ta riga tana kasancewa cikin dogon lokaci kuma akwai tutar MDD mai haske . Saboda haka wannan farmakin ba kuskure ba , tun da dadewa ne ta yi shirin kai wannan farmaki .

Wakilin rediyon kasar Sin ya aiko mana labari cewa, bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Isra'ila suka bayar a ran 2 ga watan nan , an ce, a wannan rana Majalisar ministocin Isra'ila ta zartas da Shirin kai farmaki ga kasar Lebanon. A ran 3 ga watan nan , Ehud Olmert , firayin ministan kasar Isra'ila ya bayyana cewa , gwamnatinsa a shirye take za a kafa wata rundunar sojojin kasashen Kungiyar Turai a kudancin yankin kasar Lebanon .

A wannan rana Mr. Olmert ya gana da Frank Steinmeier , ministan harkokin waje na kasar Jamus , inda ya ce , wannan rundunar sojojin kasashen duniya ya kamata ta girke a iyakar tsakanin kasar Isra'ila da Lebanon , kuma dole ne ta iya mallake hanyar mai sada Kasar Syria da Lebanon .

A wannan rana , Direktan Ofishin Fadar gwamnatin kasar Amurka ya bayyana cewa , kasarsa tana goyon bayan irin wannan rundunar sojojin , amma sojojin kasar Amurka ba za su shiga ciki ba .

Bisa labarin da aka bayar , an ce , majalisar ministocin Mr. Olmert za ta yi taro don tattauna matsalar yadda za a warware matsalolin . Saboda sojojin kasar Isra'ila suke jefa bom ba su bambanta mata da yara da asibiti da tashar binciken sojojin Majalisar Dinkin Duniya ba .

Masu binciken al'amarin duniya suna ganin cewa, bisa halin da ake ciki yanzu , an ce , ko shakka babu Mr. Olmert zai sami la'anci daga galibin kasashen duniya da kungiyoyin duniya da sassan Majalisar Dinkin Duniya da mutanen Isra'ila da kasar Lebanon . Kasar Isra'ila ba za ta wanke laifinta ba . Kamata ya yi ta dauki nauyinta dake wuyanta saboda wannan farmakin ya haddasa.(Ado)