Ran 5 ga wata, mataimakin shugaban hukumar likitocin dabbobi ta ma'aikatar aikin noma ta kasar Sin Mr. Li Jinxiang ya bayyana cewa, ma'aikatar aikin noma ta kasar Sin ta hada gwiwa sosai da kungiyoyin kasa da kasa da ma'aikatan kiwon lafiya na kasashen da abin ya shafa wajen shawo kan annobar murar tsuntsaye, sun yi musayar bayanai yadda ya kamata, sakamakon da ta samu ya sami amincewa daga kasashen duniya.
A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi a nan Beijing, Mr. Li ya yi bayanin cewa, ma'aikatar aikin noma ta kasar Sin ta sanar da kungiyoyin kasa da kasa da kasashen da abin ya shafa kan halin da take ciki a sakamakon barkewar annobar murar tsuntsaye a kasar, da kuma sakamakon sa ido da bincike da kuma yadda ta daidaita barkewar wannan annoba.(Tasallah)
|