Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-05 17:11:33    
Cin abincin da ke kunshe da zaki kadan zai iya rage kiba da kuma yawan kitsen da ke taruwa a jijiya

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani cewa, cin abincin da ke kunshe da zaki kadan zai iya rage kiba da kuma yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani a karkashin lakabi haka: yadda ya kamata a magance da kuma warkar da shanyewar kwakwalwa. To, yanzu ga bayanin.

Bisa wani nazari da manazartan kasar Australia suka yi, an ce, cin abincin da ke kunshe da zaki kadan zai ba da taimako wajen rage kiba fiye da kima da kuma yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, wanda zai haddasa ciwon zuci da shanyewar jiki.

Bisa labarin da mujallar "sabbin masu ilmin kimiyya" ta bayar a ran 25 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki, mutane 189 da shekarunsu ya kai 18 zuwa 40 da haihuwa wadanda suke da kiba fiye da kima sun shiga wannan nazarin da jami'ar Sydney ta kasar Australia ta shirya. A cikin nazarin da ya shafe makwanni 12 ana yinsa, wadannan mutane sun zabi daya daga cikin abinci iri hudu da ke kunshe da kitse da zaki kadan don ci. Abinci iri na farko shi ne wanda ke kunshe da abinci mai bayar da karfi ga jiki amma zaki kadan, iri na biyu shi ne wanda ke kunshe da abinci mai bayar da karfi ga jiki kuma zaki da yawa, iri na uku shi ne wanda ke kunshe da abinci mai gina jiki kuma zaki da yawa, iri na hudu shi ne wanda ke kunshe da abinci mai gina jiki amma zaki kadan.

Bayan da suka ci wadannan abinci iri hudu har watanni uku, nauyin jikin dukkan mutanen da suka shiga nazarin ya ragu, wanda ya kai kashi 4.2 zuwa 6.2 cikin dari na nauyin jikinsu gaba daya. Amma abincin da ke kunshe da zaki kadan ya sa kitsen de ke cikin jikin mutane ya ragu kadan idan an kwatanta shi da na sauran mutane. Alal misali, yawan kitsen da ke cikin jikin mutanen da suka ci abinci iri na farko ya kara raguwa da kashi 80 cikin dari bisa na mutanen da suka ci abinci iri na biyu. Haka kuma abinci daban daban sun ba da tasiri daban ga kitsen da ke taruwa a jijiya. Alal misali, mutanen da suka ci abici iri na farko ne kitsen da ke taruwa a jijiyarsu ya ragu sosai, sa'an nan kuma mutanen da suka ci abinci iri na uku kitsen da ke taruwa a jijiyarsu ya karu.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, yadda ya kamata a magance da kuma warkar da shanyewar kwakwalwa.(Kande)