Ran 4 ga wata, a birnin Tehran, ministan tsaron kasar Iran Mr. Mostafa Mohammad Najjar ya bayyana cewa, a zahiri kuma, barazanar sanyawa kasar Iran takunkumi yaki ne kawai da kasashen yamma suka yi ta hanyar yin amfani da tunanin jama'a, haka kuma, furofagandar banza ce kawai da suka yi. Ya kuma jaddada cewa, kasar Iran ba ta tsoron dukan takunkumi a fuskar aikin soja ba, saboda ta riga ta fuskanci takunkumi iri daban daban. A sai daya kuma, ya yi wa kasar Amurka gargadi cewa, kada ta kutsa kai cikin kasar Iran.
A wannan rana kuma, a Doha, hedkwatar kasar Qatar, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr. Kofi Annan da ke ziyarar yankin Gabas ta Tsakiya ya bayyana cewa, hanya mafi kyau da za a bi wajen warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ita ce yin shawarwari, ta da hargitsi ba zai amfanawa halin da kasar Iran da wannan yanki ke ciki ba, ya zuwa yanzu kwamitin sulhu yana yin kokari wajen magance rikici.(Tasallah)
|