Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-05 17:08:27    
Kamfanonin kasar Sin sun shiga cikin kasuwar kiwon lafiya ta kasar Afrika ta kudu

cri

Daga ranar 29 zuwa ta 31 ga watan jiya, an shirya taron kiwon lafiya na shekara-shekara a karo na biyu a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu. A gun taron, an shirya bikin nune-nunen kayayyakin kiwon lafiya, masu halartar taron sun mai da hankali sosai a kan kamfanonin kasar Sin.

A gun bikin nune-nunen kayayyakin kiwon lafiya, Afirka ta kudu da Massar da Kenya da dai sauran kasashen Afirka da kasar Amurka da Faransa da Hungary da India da Pakistan da Sin sun nuna kayayyakinsu, amma yawan na'urorin kiwon lafiya da kamfanonin kasar Sin suka nuna ya kai sulusi. Manajan hukumar kasuwa ta kamfanin kiwon lafiya na Kangdi da ke birnin Changzhou na kasar Sin Zhou Jie ya gaya mana cewa, kamfanin ya halarci wannan taro ne domin sanin manufofin kasar Afirka ta kudu game da yadda za a shiga cikin kasuwar kiwon lafiya a kasar, kuma kamfanin yana son yi musanyar ra'ayoyinsu da hukumomin kiwon lafiya na kasar. Ya ce, yana sanya ran alheri a kan makomar kasuwar kiwon lafiya ta kasar Afirka ta kudu. Ya ce,

'Na farko, kasar Afirka ta kudu tana samun bunkasuwar tattalin arziki lami lafiya, kuma tana da fasahohin kiwon lafiya masu kyau, yawan mutanen kasar ya kai miliyan 50, miliyan 7 daga cikinsu suna samun tabbacin kiwon lafiya daga kasar Afirka ta kudu. Tare da bunkasuwar tattalin arzikin kasar, yawan mutane da suke samun jin dadin kiwon lafiya daga kasarsu zai karu sosai. Sabo da haka, kasuwar kiwon lafiya ta kasar Afirka ta kudu tana da babban boyayyen karfi.'

Wata 'yar kasar Afirka ta kudu mai suna Lizl De Klerk da ta halarci taron ta gaya mana cewa, a cikin 'yan shekarun nan, kamfanonin kasar Sin suna kara shiga cikin kasuwar kiwon lafiya ta kasar Afirka ta kudu, mutanen wurin kuma suna kara mai da hankali a kan kayayyakin kiwon lafiya na kasar Sin. Ta ce,

'Ya zuwa yanzu, kasar Afirka ta kudu ta riga ta sayi kayayyakin kiwon lafiya da yawa daga kasar Sin. Mu fi mai da hankali a kan ingancin kayayyakin a maimakon wanda ya kera su. Kasar Afirka ta kudu ita ba wata kasa mai sukuni ba ne, sabo da haka mu fi son kayayyaki masu inganci kuma da araha, a kan haka kasar Sin ta taimake mu sosai.'

To, jama'a masu karanta shafin internet namu, a makon gode za mu ci gaba da ba ku wani bayani dangane da haka.(Danladi)