A ran 4 ga wata, firayin ministan kasar Jordan Marouf Bakhet ya kai suka bisa bude wutar da aka yi wa 'yan yawon shakatawa na kasashen waje a ran nan da safe.
Mr Bakhet ya ce, wannan mataki da aka dauka yana barazana ga zaman lafiyar kasar Jordan, kuma ya harzuga jama'ar kasar Jordan.
Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu hukumomin da abin ya shafa suna bincike a kan wannan lamari, ya yi imani cewa, za a gano ko wane ne ke hannu a cikin wannan danyen aiki.
Bisa labarin da muka samu, an ce, a ran 4 ga wata a wurin da ke dab da tsohon dakin wasannin kwayikwayo a birnin Amman, wani 'dan kasar Jordan ya bude wuta ga wata tawagar 'yan yawon shakatawa na kasashen waje, wannan ya sa wani 'dan yawon shakatawa na Britaniya ya mutu tare da sauran 'yan yawon shakatawa 5 da wani 'dan sanda suka ji rauni.
Kakakin gwamnatin kasar Jordan Hanna Nasser ya bayyana cewa, bude wutar da aka yi wa 'yan yawon shakatawa na kasashen waje a ran 4 ga wata a birnin Amman, babban birnin kasar Jordan, ba shi da nasaba da ko wace kungiya ko dakaru.(Danladi)
|