A ran 4 ga wata, babban kwamandan sojojin MDD da ke kasar Lebanon Alain Pelligrini ya bayyana cewa, yanzu an riga an kama hanya daidai domin ganin kasar Isra'ila ta yanje sojojinta daga kudancin kasar Lebanon.
Bisa shirin da Mr Pelligrini ya yi, manyan wakilan sojojin Isra'ila da Lebanon sun yi shawarwari a ranar a hedkwatar rundunar sojojin MDD da ke dab da tashar jirgin ruwa ta Naqoura a kudancin kasar Lebanon, inda suka tattauna a kan Isra'ila da ta janye sojojinta daga kudancin kasar Lebanon da sojojin MDD da kuma girke sojojin gwamnatin kasar Lebanon a yankin a kudancin kasar Lebanon da dai sauransu.
A ran 4 ga wata a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, babban sakataren MDD Kofi Annan, wanda yake ziyara a kasar, ya bayyana cewa, Isra'ila da kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon sun riga sun yarda da karbar aikin samun sulhuntawa da MDD ta yi musu domin kungiyar Hezbullah ta saki sojojin Isra'ila da ta kama ita kuma Isra'ila ta saki fursunonin Lebanon da ta tsare.(Danladi)
|