Sakamakon bincike mai dumi-dumi da aka bayar ya nuna cewa, har zuwa karshen shekarar 2005 da ta gabata, yawan tsoffi da shekarunsu ya wuce 65 ya zarce miliyan dari 1 a kasar Sin, wanda ya kai kashi 7.7 cikin dari bisa na jimlar yawan mutanen kasar.
Masana sun yi nazari cewa, nan gaba yawan tsoffi zai ci gaba da karuwa a kasar Sin, zaman al'ummar kasar zai kara daukan babban nauyi bisa wuyansa. Irin wannan ci gaba ya kawo wa kasar Sin barazana mai tsanani wajen ba da tabbacin zaman al'umma a nan gaba.(Tasallah)
|