A ran 4 ga wata a birnin Beijing, shugaban hukumar kimiyya da fasaha dangane da tekunan kasar Sin Sun Jiahui ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara yin binciken kimiyya da fasaha dangane da tekuna don sa kaimi ga kara saurin binciken albarkatun teku da yin amfani da su.
Bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta harba kumbuna da yawa domin sa ido a kan tekunan kasar Sin. Ban da wannan kuma, hukumomin da abin ya shafa za su yi amfani da albarkatun tekuna bisa babban mataki tun da wuri, kuma za a kara sa kaimi ga bunkasuwar sha'anonin yin magunguna da abinci dangane da tekuna, ta yadda tekuna za su kara ba da tabbaci ga kasar Sin a kan makamashi.(Danladi)
|