A ran 4 ga wata, Mr. Qu Tanzhou, direktan ofishin binciken yankunan da ke kuriyar duniya na hukumar kula da harkokin teku ta kasar Sin ya sanar wa wakilinmu cewa, tun daga shekara mai zuwa, kasar Sin za ta kafa tashar bincike ta 3 a yankin kankara da ke nahiyar kuriyar duniya ta kudu.
An bayyana cewa, za a kafa wannan sabuwar tashar bincike a wuri mafi tsayi a yankin kankara da ke kuriyar duniya ta kudu. Tsayinta daga leburin teku zai kai fiye da mita 4000. Yanayin wannan wuri yana cikin hali mai tsanani, ana kiran shi "Wurin da ba a iya taba shi ba".
Mr. Qu ya ce, kasar Sin ta zabi wurin mafi tsayi da ke yankin kankara domin kafa tashar bincike, wannan yana almantar cewa, kasar Sin ta far shiga zurfaffen yankin nahiyar kuriyar duniya ta kudu daga yankunan da ke kewayen nahiyar, wannan yana kuma almantar cewa kasar Sin ta shiga sabon mataki wajen binciken kuriyar duniya ta kudu. (Sanusi Chen)
|