Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-04 16:38:00    
Kasar Rasha tana karfafa dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da kasashen Afirka

cri
Tun daga ran 5 ga watan Satumba da muke ciki, shugaba Vladimir Putin zai fara yin ziyaya a kasar Afirka ta kudu da kasar Morocco. Wannan shi ne karo na biyu da Mr. Putin zai kai wa kasashen Afirka ziyara bayan da ya kai ziyara a kasar Aljeriya a watan Maris na shekarar da muke ciki. Wannan kuma shi ne karo na biyu da shugaban kasar Rasha zai kai wa kasashen Afirka ziyara bayan da aka rushewar Tarayyar kasashe ta Soviet. Me ya sa Mr. Putin ya kai wa kasashen Afirka ziyarce-ziyarce har sau da yawa a cikin shekara daya kawai? Ko wannan yana nuna almantar cewa yanzu kasar Rasha ta fi mai da hankali kan ayyukan diplomasiyya ga kasashen Afirka? Yanzu a ina ne kasar Rasha da kasashen Afirka za su yi hadin guiwa? Yanzu ga wani bayanin da wakiliyarmu ta rubuta bayan da ta kai ziyara ga shehun malami Jiang Yi wanda ke yin nazari kan harkokin Rasha.

Mr. Jiang Yi yana ganin cewa, ko da yake wannan ne karo na biyu da Mr. Putin zai kai wa kasashen Afirka ziyara, amma har yanzu wannan ziyara tana da manufar bude sabon shafi mai ma'anar tarihi. Mr. Jiang ya ce, "Bayan rushewar Tarayyar kasashen Soviet, ta rasa kusan dukkan kasashe abokai a Afirka. A cikin wadannan shekaru da yawa da suka wuce, shugaban kasar Rasha bai taba kai wa nahiyar Afirka ziyara ko sau daya ba. Amma a watan Maris na shekarar da muke ciki, karo shi ne na farko da shugaban kasar Rasha ya kai wa kasar Afirka ziyara. Yanzu Mr. Putin zai sake kai wa kasashen Afirka ziyarar aiki. Wannan yana nufin cewa, ziyarar da Mr. Putin zai yi tana da manufar bude sabon shafi mai ma'anar tarihi kan dangantakar diplomasiyya a tsakanin Rasha da kasashen Afirka."

Sa'an nan kuma, Mr. Jiang Yi ya ce, Mr. Putin ya bude tarihin da shugaban kasar Rasha ya kai wa kasashen Afirka ziyara, kuma a cikin shekara daya kawai, ya kai wa kasashen Afirka ziyara har sau 2. Wannan jerin matakai suna da dangantaka da manufofin diplomasiyya da kasar Rasha take bi. "Bayan da Mr. Putin ya hau kan mukamin mulkin kasar Rasha, gwamnatinsa tana kokarin raya ayyukan diplomasiyya. A hakika dai, Mr. Putin yana kokari kan yadda za a nemi dama da yawa ga kasar Rasha a kan dandalin siyasa na duniya kuma da karfafa matsayin kasa mai girma da kasar Rasha take ciki. Bayan kawo karshen yakin cacar baki, kasashen Afirka sun fara samun karfi a duk duniya. Sabo da haka, yanzu, kasar Rasha ta fara mai da hankali kan kasashen Afirka, da farko dai, kasar Rasha za ta iya yin amfaninta a kasashen Afirka. Sa'an nan kuma, tana da dangantaka sosai da manufofin kara neman dama a duniya ga kasar Rasha da neman abokai da yawa da goyon baya sosai a duniya da kasar Rasha take bi."

Mr. Jiang Yi ya ce, idan an kwatanta manufofin diplomasiyya da kasar Rasha take bi da manufofin diplomasiyya da Tarayyar kasashen Soviet ta taba dauka, za a gane cewa, an riga an yi musu gyaran fuska kwarai. Wadannan kasashe biyu, wato kasar Afirka ta kudu da kasar Morocco da Mr. Putin zai kai su ziyara suna da wakilci sosai a Afirka. "Kasar Morocco tana wakiltar kasashen arewancin Afirka. Kasar Afirka ta Kudu tana da muhimmanci sosai a yankin kudancin Afirka. Wannan ya kuma bayyana cewa, kasar Rasha tana kokarin farfado da amfaninta a duk nahiyar Afirka da dandalinta na diplomasiyya."

Bugu da kari kuma, Mr. Jiang ya ce, lokacin da kasar Rasha take kokarin habaka amfaninta irin na siyasa a Afirka, tana kuma kokarin neman hadin guiwar tattalin arziki a tsakaninta da kasashen Afirka, musamman a fannonin hakar ma'adinai da masana'antun kera injuna. Sa'an nan kuma, kasar Rasha tana kokarin sayar da makamai ga kasashen Afirka. "Sayar da makamai da yake samar da kudin musanye-musanye ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Rasha, ya kuma zama wata hanyar habaka amfanin Rasha a duniya."

Mai yiyuwa ne ziyarar da Mr. Putin zai yi a kasashen Afirka wata mafari ne ga matakan diplomasiyya ga kasashen Afirka da kasar Rasha take dauka. Lokacin da kasar Rasha take samun karfi, kuma matsayin kasashen Afirka a duniya ya yi ta samun kyautatuwa, a nan gaba, za a iya kara ganin shugabannin kasar Rasha a kasashen Afirka. (Sanusi Chen)