Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-04 15:13:41    
Yadda ya kamata a magance da kuma warkar da shanyewar kwakwalwa

cri

Ciwon shanyewar kwakwalwa wani irin ciwo ne na jijiyar kwakwalwa wanda zai iya kawo barazanara mai tsanani ga lafiyar dan Adam. bayanan da abin ya shafa sun nuna cewa, a ko wace shekara, mutane miliyan 1.5 suna kamuwa da ciwon shanyewar kwakwalwa, rabi daga cikinsu za su mutu, kuma yawancin mutanen da suka yi sa'a su kubuta daga ciwon za su rasa kwarewar aiki. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan yadda ya kamata a magance shanyewar kwakwalwa da kuma dabarun zamani na warkar da ciwon.

Malam Wang Qinmei da shekarunsa ya kai 65 da haihuwa har kullum yana cikin koshin lafiya, kuma bai taba kamuwa da ciwace-ciwace masu tsanani ba. A wata rana da safe ta lokacin bazara na shekarar da muke ciki, Mr. Wang ya je kasuwa don sayon kayayyakin lambu kamar yadda ya kan yi kullum, amma kwaram ya suma. Da ya farfado, nan da nan ne ya roki mutane da su dauke shi zuwa asibiti.

A cikin asibiti, ba da dadewa ba likita ya tabbatar da ciwon da ya kamu, Wang Jun, likita na asibiti mai lamba 301 na sojojin kasar Sin ya bayyana cewa,

"muka yi masa wani bincike kan jijiya wanda ake kiransa CTA, daga baya muka iske da cewa, wata muhimmiyar hanyar jini da ke cikin wuyarsa ta matsa sosai, har fadin hanyar jini ya kai kashi 10 cikin dari bisa hanyar jini da yadda ya kamata."

Matsewar hanyar jini da ke cikin wuya shi ne muhimmin sanadin haifar da ciwon shanyewar kwakwalwa iri na rashin jini. Mutanen da yawansu ya kai kashi 60 cikin dari na dukkan masu kamuwa da ciwon shanyewar kwakwalwa iri na rashin jini sun kamu da ciwon ne sabo da matsewar hanyar jini da ke cikin wuya. Idan hanyar jini da ke cikin wuya ta kara matsewa, to ciwon zai kara tsananta, a karshe dai za a haifar da shanyewar kwakwalwa mai tsanani.

Ban da ciwon shanyewar kwakwalwa iri na rashin jini, akwai wani iri daban wanda ake kiransa ciwon shanyewar kwakwalwa iri na fitar da jini. Muhimmin sanadin haifar da ciwon shi ne hauhawar jini, wadda ya sa kananan hanyoyin jini da ke cikin kwakwalwa su kan huje da kuma fitar da jini, sa'an nan za a haddasa shanyewar kwakwalwa.

Kafin aka kamu da ciwon shanyewar kwakwalwa, kullum akwai wasu alamu. Li Baomin, likita na asibiti mai lamba 301 na sojojin kasar Sin ya gaya mana cewa,

"kafin aka kamu da ciwon shanyewar kwakwalwa, a kan ji ciwon kai, ba a iya yi magana yadda za a fahimce shi ba, kuma hannu da kafa su kan shanye. Idan an gamu da wadannan alamu, to dole ne a mai da hankali sosai kan lafiyar jikinsa."

Game da ciwon shanyewar kwakwalwa, a da, a kan yi wa masu kamuwa da ciwon tiyata don warkar da su, amma yanzu akwai wata dabara mafi amfani da sauki wajen warkar da ciwon shanyewar kwakwalwa, wato an yi tiyata amma tare da karamin tabo. A kan samu wani wuri mai dacewa a cikin hanyoyin jini na mutane, kullum a kan zabi hanyar jini da ke cikin cinya, daga baya kuma an sa wani karamin bututu a cikin wannan hanyar jini domin warkar da ciwon. Sabo da fadin madawwarin babbar hanyar jini da ke cikin jikin mutane ya kai 15 mm, amma fadin madawwarin batutu bai kai 2mm ba, shi ya sa ba za a ji zafi ba yayin da bututu ke cikin hanyar jini.

An warkar da ciwon shanyewar kwakwalwa da Wang Qinmei ya kamu da wannan dabara. Litika ya ajiye wani kayan musamman a wurin da ke da matsi a cikin hanyar jini domin kumbura hanyar jini. Mr. Wang ya gaya mana cewa,

" lokacin da likita ya ajiye wannan kayan musamman, nan da nan ne na ji jini ya gudanar yadda ya kamata, kuma ban suma ba, jikina ya sami sauki."

Sabo da ba a bukatar mutanen da suka kamu da ciwo su shan maganin sa barci ba yayin da ake warkarda su da dabarar yin tiyata tare da karamin tabo, shi ya sa bayan awoyi 24 da aka yi tiyata, sun iya yawo, kuma bayan kwanaki hudu, sun iya fitar da kansu daga asibita. Yanzu mutane masu yawa suna so su zabi dabarar don warkar da ciwon da suke kamuwa.(Kande Gao)