Za mu bayyana muku wata karamar kabilar kasar Sin, wato kabilar E Wenke kamar yadda muka saba yi. Sannan kuma za mu bayyana muku wani bayani kan yadda ake samun sauye-sauyen zaman rayuwar jama'ar jihar Tibet sakamakon kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet.
Mutanen kabilar E Wenke wadanda suke da zama a wurare daban daban suna da suna iri iri a cikin tarihi. An taba kiransu kabilar Solun, ko kabilar Tonggus ko kabilar Yakut da dai sauransu. A shekarar 1957, bisa ra'ayoyinsu, an dayanta sunan kabilar, wato an kira ta kabilar E Wenke. Ma'anar wannan suna ita ce, mutane wadanda suke da zama a cikin gandun daji. Yawancinsu suna da zama a jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta da lardin He Longjiang. Yawan mutanen kabilar E Wenki ya kai dubu 30 da dari 5 da biyar a shekara ta 2000, kuma suke da zama tare da sauran kabilun kasar Sin. Suna amfani da yaren E Wenke, amma babu kalma.
Domin mutanen kabilar E Wenke suna zauna a wurare daban-daban, sharudan halittu na wurare suna da bambanci. Sabo da haka, tattalin arziki da zaman al'umma na kabilar E Wenke suna kuma da bambanci. Mutanen kabilar wadanda suke da zama a gandummar kabilar E Wenke mai cin gashin kanta da gandummar Chanbar ta jihar Mongoliya ta gida sun kai kashi fiye da hamsin daga cikin dukkan yawan mutanen kabilar E Wenke ta kasar Sin. Muhimmiyar sana'ar da suke yi ita ce sana'ar kiwon fatauci, kuma ba su yi zama a wani wuri kawai ba, sun yi kaurawa kullum.
Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, jama'ar kabilar E Wenke sun sha wahalolin zaman rayuwarsu sosai. A shekarar 1931, yawan mutanen kabilar da suke da zama a yankunan bakin kogin Hui ya kai fiye da dubu 3. Amma ya zuwa shekarar 1945, yawansu ya kai dubu 1 da wani abu kawai sakamakon manufar kare dangi da sojojin Japan wadanda suka kawo hari kan kasar Sin suka dauka tare da annobar ciwon inna da na sanyi da dai sauransu. Bugu da kari kuma, kafin shekarar 1945, kusan dukkan mutanen kabilar E Wenke jahilai ne. Amma yanzu, dukkan yaran kabilar sun samu izinin shiga makarantun firamare. A gandummar kabilar E Wenke, akwai makarantun sakandare 18, wasu samarin kabilar sun ci jarrabawa sun samu izinin shiga jami'o'i. Bugu da kari kuma, an riga an tsara tsarin samar da jiyya ga mutanen kabilar E Wenke a yankunan da suke da zama.
Mutanen kabilar E Wenke suna da adabin jama'a iri iri ciki har da tatsuniyoyin tarihi da irin na dodanni da karin magana da kacici-kacici.
Bisa al'adar kabilar E Wenke, wani namiji ya iya auren mace daya. An yarda da samarin kabilar E Wenke da su yi aure da samarin kabilun Mongoliya da Elunchun da na Daoer.
Ba ma kawai mutanen kabilar E Wenke suna aikin wur jan jan da kwar jini ba, har ma suna da biyayya da kirki. Babu barawo ko daya a cikin mutanen kabilar E Wenke. Maharba da makiyaya su kan gina dakuanan ajiye abinci da tufafi da kayyayakin aiki, amma ba su kulla irin wadannan dakuna ba. Idan wani mutum ya shiga cikin halin rashin abinci da tufafi a kan hanyar zuwa wani wuri, ya iya shiga kowane dakuna 2 domin neman abubuwan da yake bukata. Mutanen kabilar E Wenke suna da biyayya sosai. Lokacin da karami ya gamu da baba, dole ne ya gai da baba, kuma ya mika wani taba ga baba. Idan akwai bako ya je wani gidan kabilar E Wenke, abin mai farin ciki ne.(Sanusi Chen)
|