Ran 2 ga wata, a birnin Lome, hedkwatar kasar Togo, lokacin da yake zantawa da manema labaru, ministan kula da horar da matasa na kasar Mr. Gilbert Kodjo Atsu ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Togo ta dora muhimmanci kan batun matasa, ta mayar da aikin warware mastalar samun aikin yi da matasa ke fama da ita a gaban kome, ta kuma sami sakamako.
Mr. Atsu ya kara da cewa, matasa muhimmin kashi ne da ke cikin al'ummar kasar Togo. Saboda haka, yau da misalin shekara 1 da ta gabata, gwamnatin kasar ta kafa ofishin minista da ke kula da horar da matasa.
Ya ci gaba da cewa, samun aikin yi na daya daga cikin manyan batutuwan da matasan kasar Togo ke fuskanta a yanzu, shi ya sa gwamnatin kasar ta tsai da kudurin ba da taimako gare su wajen samun aikin yi ta hanyar tsara shirye-shirye kan horar da su da kuma tsugunar da su.(Tasallah)
|