Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-03 18:11:18    
Bangaren 'yan sanda na kasar Britaniya ya kama mutane 16 a cikin manyan matakai da ya dauka domin yaki da ta'addanci

cri

A ran 2 ga wata, bangaren 'yan sanda na kasar Britaniya ya tabbatar da cewa, daga ranar 1 ga wata da dare zuwa ranar 2 ga wata da alfijir, bangaren 'yan sanda na kasar Britaniya ya dauki manyan matakai domin yaki da ta'addanci a yankunan da ke gabashin birnin London da kudancinsa, haka kuma an kama mutane 14. Haka kuma, an kama mutane 2 a birnin Manchester.

A cikin sanarwar da bangaren 'yan sanda na kasar Britaniya ya bayar a ran nan, an ce, an kama wadannan mutane ne bisa laifin 'gudanar da shirya da harzuka aikin ta'addanci'. Sanarwar ta ce, aikin da wadannan mutane suka yi ba shi da nasaba da makircin tarwatsa jiragen sama daga kasar Britaniya zuwa Amurka a watan jiya, haka kuma ba shi da nasaba da farmakin ta'addanci da aka yi a ranar 7 ga watan Yuli na bara a birnin London.(Danladi)