Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-03 17:32:09    
Kungiyar EU ta bayar da makonni biyu ga kasar Iran don ta bayyana ra'ayinta a kan matsalar nukiliya

cri

A ran 2 ga wata, babban sakataren MDD Kofin Annan, wanda yake ziyara a kasar Iran, ya yi shawarwari da wakili na farko na kasar Iran mai kula da shawarwari a kan nukiliya Ali Larijani. Bayan shawarwarinsu, Mr Annan ya ce, sun yi shawarwari ne cikin yakini, wannan zai amfana wa aikin da zai gudanar a nan gaba.

Mr Larijani ya ce, a cikin shawarwarin da suka yi, bangarorin biyu suna ganin cewa, yin shawarwari zai zama hanya mafi kyau da ake warware matsalar nukiliya ta kasar Iran. Ya ci gaba da cewa, Mr Annan yana da ra'ayi mai yakini a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran, sabo da haka, Iran za ta nuna goyon baya gare shi.

Bisa wani labari daban da muka samu, an ce, a ran 2 ga wata, kwarya-kwaryar taron ministocin harkokin waje na kungiyar EU ya yanke shawara cewa, kungiyar EU ta bayar da makonni biyu ga babban wakilin kungiyar mai kula da manufofin diplomasiyya da zaman lafiya Javier Solana don ya yi shawarwari da kasar Iran, ta yadda za a bayyana ra'ayin kasar Iran a kan dakatar da tace sinadarin Uranium. Mr Solana zai yi shawarwari da Mr Larijani a makon gobe.(Danladi)