A ran 2 ga wata, wani jami'in gwamnatin Iraki ya ce, a ran 1 ga wata, hukumar soja ta Amurka da ke Iraki ta mika wa ma'aikatar shari'a ta Iraki ikon sarrafa gidan kurkuku.
A ranar Asabar, yau, kakakin gwamnatin Iraki Ali al-Dabbagh ya gaya wa manema labaru cewa, lokacin da tsohuwar gwamnatin da hukumar soja ta Amurka da ke Iraki suke sarrafa gidan kurkuku na Abu Ghraib, an taba haddasa matsalar lalata hakkin dan Adam a cikin wannan gidan kurkuku. Wannan gidan kurkuku ya kusan yi kama da ma'anar wulakanta fursunoni. Bayan isowarsa a cikin hannun gwamnatin Iraki, za a tsai da kudurin yadda za a yi amfani da wannan gidan kurkuku bisa moriyar kasar.
Malam Dabbagh ya ce, an riga an share wannangidan kurkuku a barkatai a kwanan baya, yanzu babu kowane fursuna yake cikin gidan kurkuku na Abu Ghraib. (Sanusi Chen)
|