Kafofin yada labaru na kasar Senegal sun ba da labari a ran 2 ga wata cewa, an samu fashewar wata mota ta kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa a lardin Casamance da ke kudancin kasar Senegal a ran 1 ga wata da yamma, inda mutum daya ya rasa ransa, yayin da wasu 3 suka ji rauni.
Kakakin kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa ya bayyana cewa, yanzu kungiyar tana binciken asalin mutumin da ya mutu da wadanda suka jikata. Ya kuma tabbatar da cewa, an samu wannan fashewar mota a wurin da ke da nisan kilomita misalin 100 a tsakaninsa da birnin Ziguinchor, babban birnin lardin Casamance a kudancin kasar Senegal, amma ya zuwa yanzu ba a san dalilin da ya haddasa wannan fashewa ba tukuna.(Tasallah)
|