Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-02 19:53:21    
Aikin tsabtace ruwan dam na kwazazzabe da ke kan kogin Yangtze ya samu sakamako mai kyau

cri
Kasar Sin ta yi ta kara karfin yin rigakafin aukuwar matsalar kazamtar da ruwan dam na kwazazzabe da ke kan kogin Yangtze. Sakamakon haka, aikin tsabtace ruwan dam na kwazazzabe ya smau cigaba sosai.

Babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin ce ta bayar da wannan albari a cikin wani rahoton da ta bayar a ran 1 ga watan Satumba.

Bisa wannan rahoto, an ce, ya zuwa yanzu, an sami cigaba sosai wajen tsabtace ruwan kazamtarwa da aka fitar da shi daga garuruwa da biranen da ke bakin dam na kwazazzabe kuma da kafuwar filayen daidaita kayayyakin banza. An riga an tsabace ruwan kazamtarwa masu dimbiin yawa. Ya zuwa karshen watan Yuni na shekarar da muke ciki, an riga an gina masana'antun tsabtace ruwan kazamtarwa 18 tare da masana'antun daidaita kayayyakin banza 14 a gundummomi 13 da ke bakin dam.

Ta yadda za a daidaita kayayyakin banza da masana'antu suka yi, an riga an tsara shirin daidaita ayyukan masana'antu 70. An rufe wasu masana'antun da suke kazamtar da ruwan dam sosai. Sa'an nan kuma, sauran masana'antu sun riga sun cimma nauyin tsabtace kayayyakin banza da suka yi da aka dora musu. Yanzu sun riga sun cimma ma'aunin fitar da ruwan banza zuwa dam na kwazazzabe bayan da suka tsabtace irin wannan ruwan banza. (Sanusi Chen)