Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-02 18:36:22    
Sojojin gwamnatin Sri Lanka sun fatattaka da nutsad da jiragen ruwa 12 na kungiyar Liberatin Tigers of Tamil Eelam

cri
A ran 2 ga wata, kakakin rundunar sojan gwamnatin Sri Lanka ya bayyana cewa, a ran 1 ga wata da dare an yi kazamin yaki a tsakanin sojojin ruwa na Sri Lanka da kungiyar Liberation Tigers of Tamil Eelam mai yin adawa da gwamnatin kasar a haddin mallakar teku na arewacin Sri Lanka, inda suka fatattaka da nutsad da kananan jiragen ruwa 12 na kungiyar, kuma sun kashe dakaru fiye da 10.

Wannan kakaki ya ce, sojojin teku na Sri Lanka sun yi kazamin yaki da kungiyar Liberation Tigers of Tamil Eelam domin kare sansanonin sojojin ruwa da ke yankin teku na Jaffna da ke arewacin kasar, sun nutsad da jiragen ruwa 12 daga cikin 20 na kungiyar, kuma sun kashe dakarun kungiyar a kalla 75. Ban da wannan kuma da akwai sojojin ruwa guda 2 na Sri Lanka sun ji rauni cikin yaki, kuma an lalata jiragen ruwa guda 2 na sojojin.

Har yanzu kungiyar Liberation Tigers of Tamil Elam ba ta ba da ra'ayinta kan wannan yaki ba tukuna. (Umaru)