Ko da yake an yi fari mai tsanani a lardin Sichuan da birnin Chongqing da sauran wasu wurare masu noman hatsi na kasar Sin, amma bisa halin da ake ciki a wannan shekara a duk kasar Sin baki daya an ce, yawan hatsin da za a girba ba zai ragu sosai ba, amma mai yiwuwa ne zai yi daidai da na shekarar da ta wuce, har ma za a samu karuwa kadan.
Wani jami'in ofishin yanayin sama na aikin noma da halittu masu rai na cibiyar binciken yanayin sama ta kasar Sin shi ne ya fayyace wannan labari a ran 1 ga wata a nan birnin Beijing, inda ya ce, ko da yake an yi fari mai tsanani a shekarar nan a lardin Sichuan da birnin Chongqing da sauran wasu wuraren kasar, amma yawan hatsin da za a girba a wadannan wurare ba zai ragu sosai ba, kuma sabo da an yi girbi mai armashi a yanayin zafi na bana a kasar Sin, wato yawan hatsin da aka girba ya karu da wajen ton miliyan 7 bisa na makamancin lokaci na bara, shi ya sa wannan zai iya ba da taimako ga rage yawan hatsin da aka yi hasararsu sabo da bala'in fari, ta yadda za a sa yawan hatsin da za a samu a duk shekarar nan a kasar Sin zai kai matsayi na shekarar bara, har ma mai yiwuwa ne za a samu karuwa kadan. (Umaru)
|