Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-02 17:25:22    
Wang Gengnian ya gana da shugabannin Rediyon Golos Rossii da kamfanin Itar-Tass News Agency na kasar Rasha

cri
A ran 1 ga watan Satumba, Wang Gengnian, shugaban Rediyon kasar Sin wanda ke yin ziyara a birnin Moscow ya gana da Okanesian Armen Garnikovich, shugaban Rediyon Golos Rossii, da Carmalito, babban edita na sashen ba da labaru na kamfanin Itar-Tass News Agency na kasar Rasha bi da bi.

A lokacin da Mr. Wang yake ganawa da Mr. Carnikovich ya ce, tun dogon lokacin da ya wuce, Rediyon kasar Sin da Rediyon Golos Rossii sun yi hadin gwiwa mai amfani kuma irin na hakika a tsakaninsu. Ya bayyana cewa, za a gina Rediyon kasar Sin da zai zama dandalin watsa labaru na kafofi da yawa bisa harsashin inganta aikin watsa labaru mai samfirin SW, sa'an nan kuma zai kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsa da kafofin watsa labaru na kasashen duniya domin kara karfinsa na yin gasa.

A lokacin da Mr. Wang yake ganawa da Carmalito, babban edita na sashen ba da labaru na kamfanin Itar-Tass News Agency, wato abokin hadin gwiwa na Rasha wajen "ziyarar sada zumunci tsakanin Sin da Rasha", ya ce, an yi hadin gwiwa mai kyau tsakanin Rediyon kasar Sin da kamfanin Itar-Tass News Agency cikin "ziyarar sada zumunci tsakanin Sin da Rasha". Kasar Sin tana fatan Rasha za ta aika da 'yan jaridunta zuwa kasar Sin domin neman labaru a lokacin "shekarar kasar Sin" ta shekara mai zuwa . (Umaru)